Kashim Shettima Ya Nemi Afuwa Kan Kalaman Da Ya Yi, Ya Ce Ba a Fahimci Abinda Yake Nufi Ba Ne

Kashim Shettima Ya Nemi Afuwa Kan Kalaman Da Ya Yi, Ya Ce Ba a Fahimci Abinda Yake Nufi Ba Ne

  • Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bai wa Musulmin Najeriya haƙuri bisa kalamansa da suka janyo zazzafar muhawara
  • Shettima ya bayyana cewa ba a fahimci kalaman nasa ba ne, amma ba wai yana nufin ya aibata addininsa ba ne
  • Shettima ya kuma bayyana cewa shi ma asalinsa Musulmi ne kuma ɗan gidan malamai, saboda haka ba zai yi kalaman da zasu tozarta addinin ba

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya fito ya bai wa Musulmin Najeriya haƙuri bisa wasu kalamai da ya yi a cikin 'yan kwanakin nan.

Kashim ya yi kalaman da suka janyo zazzafar muhawara a kafafen yaɗa labarai ne a lokacin da ake shirye-shiryen gabatar da zaɓen shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya.

Kashim Shettima ya ce an yi wa maganarsa mummunar fahimta
Kashim Shettima ya ce ba a fahimci abinda yake nufi ba, ya bai wa Musulmin Najeriya hakuri. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Kalaman Kashim Shettima da suka janyo zazzafar muhawara

Kalaman na Kashim ya yi su ne akan wanda yake ganin ya fi cancanta da ya riƙe kujerar shugabancin Majalisar Dattawa tsakanin ɗan Kudu da ɗan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: APC Ta Rasa 1, Gbaja Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ba daidai ba ne wani Musulmi daga yankin Arewacin Najeriya ya fito ya ce zai nemi kujerar shugabancin Majalisar Dattawan.

A cewar Shettima ba daidai ba ne ace shugaban ƙasar Najeriya Musulmi, mataimakinsa Musulmi, sannan kuma azo a ce shugaban Majalisar Dattawa, wanda shi ne lamba ta 3 a ƙasa ya kasance Musulmi.

Shettima a wajen taron ya ƙara da cewa a shirye yake ya durƙusa ya roƙi sanatoci masu zuwa kan su marawa ɗan takarar APC, Godswill Akpabio baya.

A kalamansa kamar yadda This Day ta wallafa:

“Mafi lalacewar Kiristan kudu, ya fi Musulmin Arewa na ƙwarai cancantar zama shugaban Majalisar Dattawan.”

A hirarsa da sashen Hausa na BBC, Shettima ya bayyana cewa mutane ba su fahimci a muhallin da ya yi maganar ta sa bane, sun mata mummunar fahimta.

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Kar Wanda Ya Ga Laifina Idan Sabon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bai Wa Yan Najeriya Kunya

Ya ce ba shi da burin aibata addininsa, kuma ya yi kalaman ne saboda maslahar Najeriya, inda ya kuma bayyana cewa akwai bayanai na sirri da suka samu waɗanda bai dace ya fitar da su ba.

Shettima ya ce asalinsa Musulmi ne kuma ɗan gidan malamai

Shettima ya kuma jaddawa 'yan Najeriya cewa shi Musulmi ne gaba da baya, kuma ɗan gidan malamai, saboda haka ba zai yi kalaman da za su aibata addinin ba.

Sai dai Kashim Shettima ya nemi afuwar duk wani Musulmin Najeriya da waɗancen kalaman nasa suka ɓatawa rai.

Sanusi Lamido Sanusi ya yi bayani kan dalilin ziyarar da ya kai wa Tinubu

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido Sanusi a fadarsa da ke Abuja.

A yayin tattaunawar tasu, Sanusi ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ya yi na cire tallafin man fetur da aka daɗe ana kashe maƙudan kuɗaɗe ta dalilinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng