Ka Dakatar Da Shugaban INEC Kamar Yadda Ka Dakatar Da Shugaban EFCC Da INEC, Lauya Ya Fadawa Tinubu
- Olisa Agbakoba, Babban lauyan Najeriya, ya yi yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tsige Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmoud Yakubu
- Agbakoba ya yabawa shugaba Tinubu kan dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da AbdulRasheed Bawa daga shugabancin Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Ƙasa (EFCC)
- Agbakoba ya jaddada cewa dole ne shugaban INEC ya bar ofis ta hanyar yin murabus ko kuma a tsige shi domin a samu damar sake fasalin zaɓe a Najeriya
Babban lauyan Najeriya, kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), Olisa Agbakoba SAN, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya tsige shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmoud Yakubu.
Agbakoba ya yi wannan kiran ne a wani rubutu da ya fitar ta shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Babban Lauyan ya nemi Yakubu ya yi murabus
A cewar babban lauyan, dole ne shugaban hukumar ta INEC ya sauka daga muƙaminsa ta hanyar yin murabus ko a tsige shi, domin kada ya kawo cikas ga sake fasalin zaɓen Najeriya da za a yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Agbakoba, ya yabawa shugaban ƙasa kan dakatarwar da ya yi wa Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), da AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban Hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Ƙasa (EFCC).
Lauyan ya nemi Shugaba Tinubu ya rushe INEC
Ya ce:
“Ina matuƙar taya murna ga Shugaba Tinubu, bisa kawar da Emefiele da Bawa, da tallafin man fetur, da cin hanci da rashawa a ɓangaren canjin kuɗi. An yi wa cin hanci da rashawa mummunan lahani.”
“Abu na gaba shi ne, shugaban ƙasa ya rushe INEC. Kowa zai aminta da hakan ba tantama, zaɓen 2023 shi ne mafi muni a tarihinmu. Ba wai ina magana ba ne kan sahihancin sakamakon zaɓen.Yawancin sakamakon yana gaban kotu ana shari'a. Duka masu shigar da ƙara da waɗanda ake ƙara sun sha wahala a hannun hukumar INEC da ta gaza.”
"A yayin da muke jiran hukunci daga kotuna, ya kamata a fara aiwatar da gagarumin garambawul ga tsarin zaɓe, amma hakan na nufin cewa shugaban INEC zai bar ofis ta hanyar yin murabus ko kuma a tsige shi, idan ba haka ba, zai iya kawowa aikin sake fasalin cikas."
Idan za a iya tunawa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa Yakubu a matsayin shugaban INEC a watan Nuwamban 2015, domin ya gaji Attahiru Jega, wanda ya kula da zaɓen 2015.
EFCC ta sanar da sabon shugaban riƙon ƙwarya bayan dakatar da Bawa
Legit.ng a baya ta kawo muku labarin cewa Hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Ƙasa (EFCC), ta sanar da sabon shugaban ruƙo bayan dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Abdulrasheed Bawa.
Abdulkarim Chukkol, shi ne wanda zai maye gurbin Bawa har zuwa lokacin da za a naɗa sabon shugaban hukumar.
Asali: Legit.ng