Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni: Mun Tika Rawa, Munyi Kamfe Don Neman Wannan Aikin, Bamu Da Dalilin Yin Guna-guni

Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni: Mun Tika Rawa, Munyi Kamfe Don Neman Wannan Aikin, Bamu Da Dalilin Yin Guna-guni

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce a matsayinsu na wadanda aka zaba basu da wani uzuri da za su ba wa 'yan Najeriya
  • Tinubu ya fadi haka ne yayin kaddamar da kwamitin tattalin arziki a ranar Alhamis 15 ga watan Yuni a Abuja
  • Ya bukaci gwamnoni da su hada kansu da kuma amfani da kananan hukumomi don inganta rayuwar al'ummarsu

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wani uzuri da za su ba wa 'yan Najeriya bayan sun zabe su kan karagar mulki.

Tinubu ya fadi hakan ne ga gwamnonin kasar yayin kaddamar da kwamitin tattalin arziki na kasa wanda mataimakinsa Kashim Shettima ke jagoranta a Abuja.

Tinubu ya shawarci gwamnoni akan ayyuka ga al'umma ba tare da uzuri ba
Ba Mu Da Wani Uzuri Ga ’Yan Najeriya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ya bukaci gwamnonin su yi aiki tukuru ba tare da neman uzuri ba

Ya bukaci gwamnonin da su haka kai da kuma amfani da kananan hukumomi don inganta rayuwar jama'a.

Kara karanta wannan

Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ni da ku muka nema, munyi yakin neman zabe don kujerar, har rawa munyi don neman mulki, don haka babu wani dalili na korafi.
"Mutanen Najeriya suna bayanmu, suna bukatar sauyi, kuma sauyin gaggawa, kuna daga cikin masu ruwa da tsaki, hada kai ba laifi bane, mu hada kanmu."

Kafin kaddamar da kwamitin, shugaban ya umarci kwamitin da su samo hanyar da za a kawo sauki akan cire tallafin man fetur.

Tinubu ya bukaci kwamitin da su ba wa gwamnatinsa hadin kai don farfado da tattalin arzikin Najeriya da ya shiga walagigi.

Wannan shi ne ganawar kwamitin na farko bayan kaddamar da shi a yau.

Kwamitin ya kunshi gwamnoni 36 na Najeriya da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN da wasu zababbu daga gwamnati.

Taron ya samu halartar gwamnoni da dama daga kasar

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan CBN: Tsohon Gwamna, Masu Bankuna Da Wasu Kwararru Da Ke Sa Ran Gaje Kujerar Emefiele

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Kwara da Osun da Ekiti da Gombe da Kogi da kuma Akwai Ibom, cewar Daily Trust.

Sauran sun hada da gwamnonin jihohin Enugu da Nasarawa da Cross River da Kebbi da Benue da Sokoto da kuma Delta da sauransu, cewar rahotanni.

Bawa: Dalilai 2 Da Ake Zato Suka Sa Tinubu Dakatar Da Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Shugaban ya dakatar da Bawa ne saboda zargin badakalar makudan kudade lokacin da yake shugabancin hukumar.

Ana hasashen akwai dalilai guda biyu da suka sa shugaban dakatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.