Idris Wase: Abin Da Yasa Ban Fasa Takara Ba Duk Da APC Ta Tsayar Da Wanda Ta Ke So

Idris Wase: Abin Da Yasa Ban Fasa Takara Ba Duk Da APC Ta Tsayar Da Wanda Ta Ke So

  • Idris Wase ya ce ya yi takarar shugabancin Majalisar Wakilai ta 10 da ɗan takarar jam’iyyarsa, Tajudeen Abbas, saboda a cewarsa akwai rashin adalci a cikin jam’iyyarsa
  • Duk da shan kaye a hannun Onarabul Tajudeen Abbas, Wase ya bayyana aniyarsa ta shiga a dama da shi a duk harkokin Majalisar Wakilan ta 10
  • Wase ya taya Abbas da mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu murnar nasarar da suka samu tare da yin kira da a haɗa a tsakanin ‘yan majalisar don samun ci gaba

Abuja - Tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Idris Wase ya bayyana cewa ya yi takarar shugabancin Majalisar Wakilai ta 10 da ɗan takarar jam’iyyarsa, Tajudeen Abbas ne saboda akwai rashin adalci da rashin daidaito a jam’iyyarsa.

Wase wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Wase a jihar Filato ya sha kaye a takarar kujerar kakakin majalisar a hannun Tajuddeen Abbas mai wakiltar mazaɓar Zaria a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: APC Ta Rasa 1, Gbaja Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

Ahmed Wase ya bayyana dalilin da ya sa shi fitowa takarar shugabancin Majalisar Wakilai
Idris Wase ya ce rashin adalcin jam'iyyarsa ne ya sanya shi fitowa takarar kakakin Majalisar Wakilai. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: UGC

Rashin daidaito wajen raba muƙamai ne ya sanya ni fitowa - Wase

A wata sanarwa da ya fitar bayan kammala zaɓen, Wase ya ce jam'iyyarsa ta gaza yin adalci wajen raba muƙamai yadda ya kamata ga 'yan kowace shiyya, in ji rahoton Channels Tv.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wase ya kuma ƙara da cewa dole ne dukkan ‘yan majalisar su haɗu wuri guda don tunkarar manyan al’amuran da suka shafi haɗin kan majalisar don samun damar tafiyar da ita yadda ya kamata.

Wase ya yi kira da haɗin kan Majalisar Wakilai ta 10

Idris Wase ya kuma taya Honarabul Tajudeen Abbas da mataimakinsa Benjamin Kalu, murna bisa nasarar da suka samu ta zama Kakaki da mataimakinsa.

Sannan ya kuma yi kira ga magoya bayansa, masu yi masa fatan alheri, da sauran ’yan takarar majalisar da su zo a haɗu domin daidaiton Majalisar Wakilan ta 10.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Femi Gbajabiamila Ya Shirya Yin Murabus, Bayanai Sun Fito

Wase ya ƙara da cewa:

"Na yi alƙawarin shiga dumu-dumu cikin dukkan lamurran Majalisar wakilan ta 10, kuma zan ci gaba da wakiltar ba iya mutanen mazaɓa ta ta Wase ba, har da ma sauran 'yan Najeriya baki daya."

Tajuddeen Abbas, ya yi nasarar zama kakakin Majalisar Wakilan bayan doke Ahmed Idris Wase da kuma Aminu Sani Jaji a zaɓen da ya gabata ranar Talata.

Dalilin da ya sa 'yan Majalisar adawa suka zaɓi ɗan takarar APC a majalisar

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, ɗan Majalisar Wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Denis Agbo, ya bayyana dalilin da ya sa takwarorinsa na adawa suka zaɓi Tajuddeen Abbas, ɗan takarar APC a zaɓen Majalisar Wakilan.

Ya bayyana cewa rashin tabbacin samun haɗin kan duka 'yan majalisun adawar ne ya sa suka yanke shawarar zaɓar ɗan takarar na APC.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Yi Sabon Shugaba, Matashi Ya Lashe Kujerar Kakakin Majalisa

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng