Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Yi Zazzafan Martani Kan Binciken Da Sabon Gwamna Dauda Lawal Ke Yi Masa
- Tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya zargi gwamna Dauda Lawal da yin amfani da ‘yan sanda wajen wulakanta shi da ci masa mutuncin
- Matawalle na zargin cewa ‘yan sanda sun mamaye gidansa tare da liƙa takardar gayyata a jikin babban ƙyauren kofar gidan nasa, wanda yake ganin ya sabawa doka da ‘yancin ɗan adam
- Mashawarcin Matawalle kan harkokin yaɗa labarai, Mista Diyemi Saka ya yi ikirarin cewa bita da ƙullin da ‘yan sanda da gwamnatin jihar ke yi wa matawalle ba zai haifarwa jihar ɗa mai ido ba
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya zargi gwamna Dauda Lawal da yin amfani da ‘yan sandan jihar wajen wulaƙanta shi da kuma cin zarafinsa.
Mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Deyemi Saka ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Tashin Hankali a Gidan Gwamnatin Jihar Ondo Yayin Da Mataimakin Gwamna Ya Huro Wuta Sai An Mika Masa Mulki
Yan sanda sun liƙa takardar gayyata a jikin babban ƙyauren gidan Matawalle
Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun je gidan Matawallen, inda suka liƙa takardar gayyata a jikin kofar gidan, wanda hakan ya ce ya sabawa tsarin doka da ‘yancin ɗan adam.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saka ya buƙaci Gwamnan Zamfara mai ci, Dauda Lawal da ya kawo ƙarshen abinda ke faruwa da Matawalle, inda ya ce ci gaba da hakan, ba zai haifawa jihar ɗa mai ido ba.
Saka a cikin sanarwa da ya fitar, ya zargi ‘yan sanda da gwamnatin jihar da yi wa Matawallen bita da ƙulli.
Matawalle ya ce Dauda Lawal na ƙoƙarin wulaƙanta shi
A kalamansa:
“Muna so mu sanar da jama'a game da wannan mugun nufi da azarbabi da rundunar 'yan sandan Zamfara ke yi na aikata laifuka, wulakanci da cin zarafin Bello Muhammad Matawalle."
"Bayan mamaye gidansa ba bisa ƙa'ida ba, tare da rashin iya samunsa da laifi kan zarge-zargen da ake yi masa, rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana a gidansa, inda ta liƙa takardar gayyata a jikin babban ƙyauran gidansa."
“Wannan gayyata wani tunani ne da kuma burin Dauda Lawal na ganin ya tozarta Matawalle. Duk da cewa babu wanda ke adawa da ‘yan sandan a kan aikinsu, bita da ƙullin siyasa ka iya ƙara rura matsalar rashin tsaron da ta baibaye ko ina a faɗin jihar.”
“Har ila yau, za mu so jama’a su sani cewa wannan ba fafutukar neman yancin al’ummar Zamfara ba ne, yaƙin neman samun ƙarfin iko a jihar Zamfara ne.”
Sai dai a wani rahoto da Daily Trust ta wallafa a kwanakin baya, an jiyo sabon Gwamnan jihar ta Zamfara, Dauda Lawal na zargin tsohon gwamnan da kwashe kadarorin gidan gwamnatin jihar.
Gbajabiamila ya yi murabus daga Majalisar Wakilai
A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa a yau Laraba ne tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga kujerarsa ta Majalisar Wakilai.
Murabus ɗin Gbjabiamila na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ya bai wa majalisar, wacce kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya karanta.
Asali: Legit.ng