Majalisa Ta 10: Kar Ku Ga Laifina Idan Akpabio Ya Gaza, Sanata Ndume
- Ɗaya daga cikin jagororin kamfen Akpabio/Barau a majalisa ta 10, Sanata Ali Ndume, ya yi bayani mai jan hankali
- Ndume ya ce kar wanda ya ɗora masa laifi idan sabon shugaban majalisar dattawa ya ba mutane kunya nan gaba
- Sanatan Borno ta kudu ya bayyana cewa ya yi la'akari da kwarewar Akpabio ne shiyasa ya mara masa baya har ya ci zaɓe
Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, ya ce kar wanda ya ɗora masa laifi idan sabon shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gaza yin abinda ake tsammani.
Sanata Ndume ya yi wannan furucin ne yayin hira da Channels tv cikin shirinsu na Siyasa a Yau awanni bayan rantsar da mambobin majalisar tarayya ta 10 ranar Talata.
Idan baku manta ba Ndume na cikin waɗanda suka yi kakagida a sahun gaba wajen kamfen Akpabio da kuma mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin, gabanin zaɓe.
Jaridar Vanguard ta rahoto Ndume na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Idan daga baya ya gaza, ya zama mafi muni, kar ku ga laifina, to don me za'a ɗora mun laifi? Babu wanda na tilasta masa ya zaɓe shi. Ina da yaƙinin yafi kowa cancanta amma ban san me zai aikata ba gobe."
"Ba daidai bane (A ɗora mun laifin gazawar Akpabio), Akpabio daban ni daban domin ko a gaban Allah, Akpabio ne zai yi bayanin ayyukansa, nima na yi bayanin nawa."
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ta 9 wacce aka rushe, ya ƙara da cewa tabbas ya faɗa a baya cewa Sanata Akpabio ne ya fi dacewa da matsayin.
Meyasa Sanatan ya aminta da Akpabio?
Ndume ya yi bayanin cewa ya yi hasashen tsohon ministan Neja Delta ne ya fi cancanta bisa la'akari da abubuwan da ya gani a zahirance.
"Na san Akpabio na tsawon shekaru, a baya ya riƙe shugaban marasa rinjaye kuma a lokacin ina matsayin shugaban masu rinjaye. Na san shi mutum ne mai basira da salo kuma ba ya nuna banbancin ƙabila."
"Shi kwarwarren lauya ne, ya rike kujerar minista da Kwamishina, yana da duk wata kwarewa da gogewar yin abinda 'yan Najeriya ke tsammani."
Mambobin APC Sun Mamaye Zauren Majalisar Dokokin Jigawa Kan Zaben Kakaki
A wani rahoton na daban kun ji cewa 'ya'yan APC sun fantsama zanga-zangar adawa da wanda aka zaɓa a matsayin sabon shugaban majalisar jihar Jigawa.
Masu zanga-zangar sun nemi a bai wa wani daban matsayin maimakon Garba, wanda shi ne kakakin majalisar da ta gabata.
Asali: Legit.ng