Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10
Bayan an daɗe ana kai ruwa rana kan zaɓen shugabannin majalisa ta 10, daga ƙarshe komai ya zo ƙarshe inda aka gudanar da zaɓen a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.
An yi ta taƙaddama da muhawara bayan jam'iyyar APC ta sanar da zaɓinta na Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da Abbas Tajudeen a matsayin kakakin majalisar wakilai.
Bayan an sanar da su, ƴan majalisar sun ci gaba da yaƙin neman zaɓe ta hanyar bibiyar takwarorin su ƴan majalisa da ziyartar wasu gwamnoni musamman na APC.
Rawar da gwamnoni suka taka wajen nasarar Akpabio, Abbas
Da yawa daga cikin gwamnonin ciki har da na jam'iyyar adawa ta PDP, sun marawa ƴan takarar na APC baya, waɗanda daga ƙarshe suka samu nasara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ga jerin gwamnonin da suka halarci zaɓen shugabannin majalisar ta 10 wanda Legir.ng ta tattaro.
Babajide Sanwo-Olu
Gwamnan jihar Legas yana daga manyan ƙusoshin da suka halarci majalisar domin ganin zaɓen wanda ya samar da Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Kafin zuwan ranar zaɓen, Sanata Akpabio ya ziyarci Sanwo-Olu a Legas inda gwamnan ya nuna masa goyon bayansa kan takararsa.
Yahaya Bello
Gwamnan na jihar Kogi yana daga cikin jagororin APC da suka halarci zaɓen da ya samar da Akpabio da Abbbas a matsayin shugabannin majalisa ta 10.
Seyi Makinde
Gwamnan na jihar Oyo wanda ya kasance ɗan jam'iyyar adawa ta PDP, ya halarci zaɓen na shugabannin majalisa.
Makinde a ranar Litinin ya yi nuni da cewa da shi da takwarorinsa za su halarci zaɓen a majalisa domin sanya ido akai, inda ya ƙara da cewa ba wai domin saboda addini ba ne face sai domin yin abinda ya dace.
Akpabio Ya Nemi Muhimman Bukatu Guda 2 Wurin Tinubu
A wani labarin kuma, sabon shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya aike da wasu muhimman buƙatu a wajen shugaba Bola Ahmed Tinibu.
Shugaban majalisar dattawan ya buƙaci Shugaba Tinubu da riƙa aikewa majalisar da ƙasafin kuɗi akan lokaci domim amincewa da shi.
Asali: Legit.ng