Bodinga, Dan Shekara 47 Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Sokoto

Bodinga, Dan Shekara 47 Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Sokoto

  • Majalisar dokokin jihar Sakkwato ta zaɓi sabon kakakin majalisa da kuma mataimakinsa ranar Talata, 13 ga watan Yuni
  • Tukur Bala Bodinga, mamba mai wakiltar mazabar Bodinga ne ya samu nasarar zama sabon shugaban majalisar dokokin
  • Da yake jawabi, ya ce a karkashin jagorancinsa majalisar dokoki zata tafi da kowane mamba kuma zata taimakawa gwamnatin Sakkwato

Sokoto - Mamban majalisar dokokin jihar Sakkwato, Tukur Bala Bodinga, ɗan kimanin shekara 47 a duniya ya samu nasarar zama sabon kakakin majalisar.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gwadabawa ta kudu a inuwar APC, Bello Idris, ne ya tsayar da Honorabul Bodinga, mai wakiltar mazaɓar Bodinga a matsayin wanda ya dace ya jagoranci majalisar.

Sabon kakakin Majalisar Dokokin Sakkwato.
Bodinga, Dan Shekara 47 Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Sokoto Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa nan take Habibu Modachi, mai wakiltar mazaɓar Isa karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya miƙe ya goyi bayan Bodinga.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Yi Sabon Shugaba, Matashi Ya Lashe Kujerar Kakakin Majalisa

Daga nan baki ɗaya mambobin majalisar suka kaɗa masa kuri'unsu ba tare da hamayya ba yayin rantsarwa ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zamu yi aiki a inuwa ɗaya - Bodinga

Da yake jawabin godiya, sabon kakakin majalisar dokokin Sakkwato ya tabbatar wa abokan aikinsa cewa zai yi aiki tare da haɗin kan kowa domin ci da jihar gaba.

A kalamansa ya ce:

"Zamu tabbata mun gina majalisar dokokin da zata jawo kowa a jiki, ta haɗa kan kowane mamba da ma'aikatan majalisa wuri ɗaya a yi aiki tare."

Sabon kakakin ya ƙara da cewa shugabancinsa zai yi aiki bakin gwargwado domin taimakawa gwamnati ta cimma kyawawan manufofi da sauke haƙƙin mazauna Sakkwato.

Majalisa ta zabi mataimakin kakaki

Bugu da ƙari, mambobin majalisar sun zaɓi Kabiru Ibrahim, mamba mai wakiltar mazaɓar Kware karkashin inuwar jam'iyyar APC a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisa.

Kara karanta wannan

Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Aminu Almustapha Gobir, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni ta kudu a inuwar APC ne ya fara gabatar da shi kuma sauran mambobi suka biyo baya.

Sabon Ɗan Majalisa Ya Lashe Zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato

A wani rahoton na daban Majalisar dokokin jihar Filato ta zaɓi sabon shugaba yayin zaman rantsarwa ranar Talata, 13 ga watan Yuni.

Rahoto ya nuna cewa an ta zaɓi Honorabul Moses Sule a matsayin sabon kakakin majalisar Filato ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262