Burin ’Yan Kwankwasiya Ya Cika, Dan NNPP Ya Zama Shugaban Majalisa a Kano
- Majalisar jihar Kano ta zabi Jibrin Isma'il Falgore a matsayin kakakin majalisar ta 10 a yau Talata 13 ga watan Yuni
- Falgore wanda dan jam'iyya mai mulki ta NNPP ce ya samu amincewar Lawal Hussaini na mazabar Dala a majalisar
- Jam'iyya mai mulki ta NNPP a jihar ta na da mambobi 26 yayin da jam'iyyar adawa ta APC ke da mambobi 14
Jihar Kano - An Zabi dan majalisa da ke wakiltar Mazabar Rogo, Isma'il Jibrin Falgore a matsayin kakakin majalisar Jihar Kano ta 10.
Falgore wanda dan jam'iyyar NNPP ne ya kasance shugaban majalisar ba tare da wata adawa ba.
Jam'iyyar NNPP ita ce ke da rinjaye a majalisar da mambobi 26 yayin da jam'iyyar APC ke da mambobi 14.
Yadda Falgore ya kasance kakakin majalisar jihar Kano
Falgore wanda dan NNPP ce ya samu amincewa daga Lawal Hussaini mai wakiltar Dala a NNPP, yayin da ya samu goyon baya daga dan jam'iyyar adawa ta APC mai suna Musa Ali Kachako daga mazabar Takai a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, zababben dan majalisa daga mazabar Rimingado/Tofa, Muhammad Bello Butubutu na jam'iyyar NNPP ya kasance mataimakin kakakin majalisar ta 10, cewar rahotanni.
Butubutu ya samu amincewar Zubairu Hamza Masu na jam'iyyar NNPP daga mazabar Sumaila tare da goyon bayan dan jam'iyyar adawa ta APC daga mazabar Gwarzo.
Majalisar jihar Kano ta na da mambobi 40
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa majalisar ta na dauke da 'yan majalisu 40 da suka shigo a matsayin sabbi ko suka dawo kan kujerunsu a zaben bana.
An kuma tattaro cewa, majalisar ta wannan zangon za ta kasance ne da mambobin jam'iyyar APC 14 da kuma na jam'iyyar NNPP 26 mai mulkin jihar.
Jam'iyyar NNPP Ta Lashe Kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano
A wani labarin, jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta lashe kujero da dama yayin zaben majalisar jihar Kano.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rogo, Isma'il Jibrin Falgore ya lashe zaben majalisar dokokin a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Baturen zaben da ke ya bayyana Falgore a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris da kuri'u 18,211.
Asali: Legit.ng