Tashin Hankali a Gidan Gwamnatin Jihar Ondo Yayin Da Mataimakin Gwamna Ya Huro Wuta Sai An Mika Masa Mulki
- Lucky Orimisan Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo, ya taso gwamnan jihar Rotimi Akeredolu a gaba saboda rashin lafiyarsa
- Ana zargin Aiyedatiwa da ƙokarin tilasta gwamna Akeredolu, wanda baya da lafiya, ya miƙa masa mulki sannan ya yi murabus
- Ana kuma zargin mataimakin gwamnan na jihar Ondo da ƴada labarai kan mutuwar gwamnan satin da ya gabata
Akure, jihar Ondo - Akwai ƴar tsama a gidan gwamnatin jihar Ondo yayin da mataimakin gwamnan jihar, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, yake son gwamna Rotimi Akeredolu ya miƙa masa mulki ba tare da ɓata lokaci ba.
A cewar wani rahoto da jaridar Vanguard ta fitar ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, Aiyedatiwa shi ne ya kitsa jita-jitar da aka yi ta yaɗawa satin da ya gabata kan rashin lafiyar gwamnan da ta mutuwarsa.
Ashsha: Matawalle Ya Bayyana Irin Satar Da Gwamnatin Zamfara Ta Yi Masa a Gida Da Sunan Kwacen Motoci
Akeredolu yana sane da ƙulla-ƙullar da mstaimakin gwamnan yake yi
Aiyedatiwa ya kitsa jita-jitar ne domin mutanen jihar su goya masa baya ya samu abinda yake so.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyoyi daga cikin gidan gwamnatin jihar sun bayyana cewa Akeredolu yana sane da burin mataimakin nasa na karɓar mulki, a cewar Vanguard.
Majiyoyin sun bayyana cewa:
"Rikicin ya fara ne lokacin da gwamna Akeredolu ya tafi hutun shaƙatawa ya miƙa ragamar mulkin jihar a hannun mataimakin gwamna."
"A ɗan zaman da ya yi a matsayin gwamnan jihar, ana zargin mataimakin gwamnan da fifita son zuciyarsa akan abinda yakamata ya aiwatar a jihar."
"Wasu daga cikin ƴan majalisar zartaswar jihar sun yi zargin cewa mataimakin gwamnan ne yake da hannu akan yaɗa labaran jita-jita kan rashin lafiyar gwamnan."
A satin da ya gabata ne dai rahotannin jita-jita suka yi ta yawo kan mutuwar gwamna Akeredolu, wanda har sai da gwamnatin jihar ta fito ta musanta jita-jitar mutuwar gwamnan.
Gwamnan Katsina Ya Soke Filayen Da Gwamnatin Magabacinsa Ta Raba
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya soke filayen da gwamnatin magabacinsa ta Aminu Bello Masari ta raba a jihar.
Gwamnan ya yi wannan hukuncin ne biyo bayan yadda aka raba filayen ba bisa ƙa'idar doka ba a tsakanin wasu shugabannin ma'aikatu a jihar.
Asali: Legit.ng