Sauye-Sauye 5 Na Tinubu A Makonsa Na Biyu A Matsayin Shugaban Kasa Da Suka Girgiza Najeriya

Sauye-Sauye 5 Na Tinubu A Makonsa Na Biyu A Matsayin Shugaban Kasa Da Suka Girgiza Najeriya

Shugaba Tinubu tun a ranar 29 ga watan Mayu da aka rantsar da shi, ya fara gabatar da gagarumin aiki na farko, wato cire tallafin man fetur da 'yan Najeriya ke ta tattaunawa a kai har ya zuwa yau.

Tinubu ya ɗora a sati na biyu da ya yi a kan karagar mulki a matsayin shugaban Najeriya, ta hanyar yin wasu manyan sauye-sauye da kuma gabatar da wasu manyan ayyuka da suka ja hankulan 'yan Najeriya.

Manyan ayyukan da Tinubu ya yi a mako na biyu
Manyan sauye-sauye biyar da Tinubu ya yi a mako na biyu a ofis. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro muku manyan abubuwa biyar da suka wakana a mako na biyu na mulkin Tinubu da suka girgizar Najeriya, abubuwan su ne:

1. JOHESU ta dakatar da yajin aiki bayan ganawa da Tinubu

Daya daga cikin manya-manyan matakan da shugaba Tinubu ya ɗauka a makonsa na biyu a kan karagar mulki, shi ne ganawar da ya yi da kungiyar haɗin gwiwa ta ma'aikatan lafiya (JOHESU).

Kara karanta wannan

Kowa ya shirya: A karon farko, Tinubu zai fito ya yi wa 'yan Najeriya jawabi mai daukar hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JOHESU ta kasance tana gudanar da yajin aiki ne tun kafin hawan Tinubu kan karagar mulki.

Ganawar da aka yi tsakanin Tinubu da JOHESU, ta kai ga cimma matsayar dakatar da yajin aikin da kungiyar ta kwashe kwanaki 21 tana yi.

2. Tinubu ya sanya hannu kan ƙudirin karawa alƙalai shekarun aje aiki

Wani daga cikin manyan ayyukan da Tinubu ya gabatar a mako na biyu, shi ne rattaɓa hannu kan kudirin dokar ƙara shekarun ritayar alƙalan Najeriya daga shekaru 65 zuwa 70.

Shugaba Tinubu dai ya sanya hannu kan ƙudirin dokar, wanda majalissar wakilai ta 9 ta amince da shi a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, a wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun Abiodun Oladunjoye, daraktan yaɗa labarai na fadar Gwamnatin Tarayya.

3. Tinubu ya rattaɓa hannu kan sake fasalin gudanar da wutar lantarki

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi da ya farantawa ‘yan Najeriya rai, shi ne amincewarsa ga ƙudirin samar da wutar lantarki da ya bai wa jihohi, ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun mutane damar samarwa da kuma rarraba wutar lantarki a Najeriya.

Ƙudirin ya soke dokar sake fasalin wutar lantarki ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo (EPSRA), da aka sanya wa hannu a shekarar 2005.

4. Tinubu ya gana da Kwankwaso

Ana ganin ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da tsohon gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wani babban motsi a siyasar Tinubu tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulki.

Ana dai ganin Kwankwaso a matsayin babban abokin gabar ɗaya daga cikin na kusa da Tinubu, Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano da ya gabata.

An dai yi ta raɗe-raɗin cewa, Kwankwaso ka iya zama mamba a majalissar ministocin Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wasu Kalamai

5. Tinubu ya dakatar da Emefiele a matsayin Gwamnan CBN

Daga cikin abubuwan da Tinubu ya burge ‘yan Najeriya da su, shi ne dakatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni da ya yi.

Watanni biyu gabanin zaɓen shugaban ƙasa, Emefiele ya sauya fasalin kuɗin Najeriya ƙarƙashin tsarin sauya fasalin naira.

An bayyana cewa manufar sauya fasalin kuɗin shi ne daƙile siyan kuri’u, amma daga bisani ta ƙare kan ‘yan Najeriya da dama, wanda sai da suka koma suna siyan kuɗi da kuɗi.

Tinubu ya bayyana yadda zai sakawa 'yan Najeriya bayan cire tallafin mai

Legit.ng ta kawo muku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin sakawa 'yan Najeriya bisa wahalar da cire tallafin man fetur ta saka su a ciki.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jinjinawa tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa, Marigayi MKO Abiola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng