Majalisa Ta 10: Kashim Shettima Ya Bayyana Abinda Zai Yi Wa Zababbun Sanatoci Domin Su Zabi Akpabio

Majalisa Ta 10: Kashim Shettima Ya Bayyana Abinda Zai Yi Wa Zababbun Sanatoci Domin Su Zabi Akpabio

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana shirinsa na neman alfarma a wajen zaɓaɓɓun sanatoci domin su zaɓi Godswill Akpabio
  • Shettima ya ce a shirye yake ya durƙusa kan gwiwowinsa domin ya nemi sanatocin wannan alfarmar ta zaɓar Akpabio
  • Ya bayyana cewa akwai tagomashi sosai da ƙasar nan za ta samu idan Sanata Godswill Akpabio ya ɗare shugabancin majalisar dattawa

FCT, Abuja - Mataimakn shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya roƙi zaɓaɓɓun sanatoci da su zaɓi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10.

Shettima ya bayyana cewa a shirye yake da ya ɗuka ƙasa kan gwiwowinsa domin ya nemi wannan alfarmar a wajen zaɓaɓɓun sanatocin, cewar rahoton Daily Trust.

Shettima ya shirya dukawa saboda Akpabio
Kashim Shettima tare da Ali Ndume da Godswill Akpabio Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wajen wata liyafa da aka shirya a daren ranar Asabar, domim nuna goyon baya ga takarar Sanata Akpabio da Barau Jibrin ta shugabancin majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Kashim Shettima Ya Bayyana Dan Takarar Da Ya Cancanci Shugabantar Majalisar Dattawa

Shugabancin Akpabio zai ƙara haɗa kan ƙasa

Ya bayyana cewa ɗarewar Akpabio kan kujerar shugaban majalisar dattawa, zai samar da haɗin kai da daidaito a ƙasar nan, rahoton The Guardian ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"A shirye na ke na ɗuka kan gwiwowina na roƙi takwarorina domin su zo su yi tafiyar Akpabio saboda zaman lafiya a ƙasar nan."
"Idan aka cire ɓangaren addini, Akpabio ya cancanta kuma yana da ƙwarewar da zai jagoranci majalisar dattawa ta 10. Sannan daɗin daɗawa ya fito daga yanki mai muhimmanci sannan shi Kirista ne shi."

Mataimakin shugaban ƙasar ya tabbatarwa da zaɓaɓɓun sanatocin shirinsa ma ci gaba da ƙoƙarin ganin Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa ta hanyar neman goyon bayan waɗanda basu mara mai baya ba har ya zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Shugaba Tinubu Da Akpabio Kan Shugabancin Majalisar Dattawa

Sama da zaɓaɓɓun sanatoci 50 ne suka samu halartar liyafar tare da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Shettima Ya Bayyana Cancantar Akpabio

A wani labarin na daban kuma, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Shettima ya yi nuni da cewa Akpabio yana da ƙwarewa da gogewar da zai jagoranci majalisar dattawan yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng