Kashim Shettima Ya Ce Sanata Akpabio Ya Cancanci Jagorantar Majalisar Dattawa
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya raba gardama kan wanda ya cancanta ya shugabanci majalisar dattawa ta 10
- Shettima ya bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio shi ya cancanta ya ɗare kan kujerar saboda ƙwarewar da yake da ita
- Mataimakin na shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa suna goyon bayan Akpabio ne saboda muhimmancin yankin da ya fito da kuma addininsa
Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio, ya cancanta da ya zama shugaban majalisae dattawa.
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa mataimakin shugaban ƙasan, ya bayyana hakan ne a wajen wata liyafa da ƴan tawagar yaƙin neman zaɓen Akpabio na 'Stability Group' suka shirya a otal ɗin Transcorp Hilton a birnin tarayya Abuja ranar Asabar.
Shettima ya bayyana cewa Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC suna goyon bayan tsohon gwamnan na jihae Akwa Ibom ne, saboda ya fito daga yanki mai muhimmanci a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa sun cimma wannan matsayar ne domin ta yi daidai da yawan haɗin kan da mu ke buƙata a ƙasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Sanata Akpabio ya cancanta kuma yana da ƙwarewar da zai jagoranci majalisar dattawa ta 10."
“Sannan daɗin daɗawa ya fito daga yanki mai matuƙar muhimmanci sannan kuma kirista ne."
Shettima ya bayyana aikin da ke gaban jam'iyyar APC
Shettima ya bayyana cewa jam'iyyar APC tana da buƙatar nuna kanta a matsayin jam'iyya wacce ta ke maraba da kowace ƙabila da kowane addini.
"Dogarina Inyamuri ne wanda mu ka yi aiki tare da shi tun lokacin ina gwamna. Ya kasance jami'ai mai kwazo da jajircewa, har a cikin lokacin da hare-haren Boko Haram suka yi ƙamari a jihar Borno." A cewarsa.
A ranar Talata ne dai mai zuwa majalisar dattawan za ta zaɓi shugabannin da za su jagoranceta nan da shekara huɗu masu zuwa.
Dattawan Arewa Sun Shawarci APC
A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar dattawa Arewa ta shawarci jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kada ta yi katsalandan wajen zaɓen shugabannin majalisa ta 10.
Ƙungiyar ta shawarci APC da ta bar zaɓaɓɓun ƴan majalisar su zaɓi ƴan takarar da suka kwanta musu a rai a lokacin zaɓen shugabannin majalisar da ke tafe.
Asali: Legit.ng