"Kar Ki Tsoma Baki a Zaben Shugaban Majalisar Dokokin Tarayya", Dattawan Arewa Ga APC
- Dattawan arewa sun bukaci jam'iyyar APC mai mulki da ta ba zababbun yan majalisa dama su zabi wanda suke so ya shugabance su
- Ango Abdullahi ya ce ya zama dole kowa ya bi kundin tsarin mulkin kasar yadda yake wanda ya kuma yi bayani kan yadda za a gudanar da lamuran majalisar wacce ke cin gashin kanta
- Wannan kira na zuwa ne yayin da yan takarar kujerar shugabancin majalisar ke zawarci takwarorinsu domin su zabe su gabannin rantsar da majalisar ta 10 a ranar Talata mai zuwa
Kungiyar dattawan arewa (NEF) ta shawarci jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ta bari yan majalisar dokoki ta 10 su zabi wanda suke so ya jagoranci harkokinsu.
Jagoran kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa ya kamata yan majalisar su zabi shugabanninsu daidai da yancin kowani bangare na gwamnati.
Shugaban Majalisar Dattawa: "Zaman Lafiyar Najeriya Ya Fi Aljihunmu Muhimmanci", Shettima Ga Sanatoci
Legit.ng ta rahoto cewar za a rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.
Abdullahi said the members-elect should be left alone to decide who their leaders will be because they have clear rules they must work with.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abdullagi ya ce ya kamata a kyale zababbun yan majalisar su yanke shawara kan su wanene za su zama shugabanninsu saboda suna da tsari da dole su yi aiki da shi, rahoton Ripples Nigeria.
Ya ce:
"Tushen tsarin shine kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya fito karara ya bayyana cewar za a samu irin wannan majalisa da kuma yadda za a kafa ta da kuma samar da shugabancinta. A iya saninmu, ya kamata ace duk wani da abun ya shafa ya bi kundin tsarin mulki yadda yake.
"Za Ka Koya Mun Yadda Ake Komawa Majalisa Ba Tare Da Zaben Fidda Gwani Ba", Okorocha Ya Yi Shagube Ga Lawan
"Jam'iyya mai mulki ba ita ke da iko kan majalisar dokokin tarayya, wacce ta kasance majalisa mai zaman kanta ba."
Shugaban majalisar dattawa: Shettima ya yi gagarumin jan hankali ga zababbun sanatoci
A wani labarin kuma, mun ji cewa gabannin rantsar da zauren majalisa ta gaba, mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bukaci zababbun sanatoci da su yi aiki da hankali wajen zabar shugabannin majalisar mai zuwa.
Majalisar dattawa za ta zabi shugabanninta na majalisa ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.
Da yake magana yayin zaman rufe majalisar dattawa ta tara a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, Shettima ya fada ma yan majalisar cewa zaman lafiyan kasar ya fi cika aljihunsu daraja, jaridar The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng