Shugaban Majalisar Dattawa: Yan Majalisa Na Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka - Rahoto

Shugaban Majalisar Dattawa: Yan Majalisa Na Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka - Rahoto

  • Kujerar shugaban majalisar dattawa na iya zuwa ga wanda ya saki bakin aljihu gabannin bikin rantsar da majalisar a ranar 13 ga watan Yuni
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yan majalisa a zauren majalisar dattawan na iya siyar da kuri'unsu kan $5,000, $10,000 ko fiye da haka
  • Yanzu tseren na a tsakanin Sanata Orji Kalu, Sanata Abdulaziz Yari da Sanata Godswill Akpabio

Wani sabon bayani ya billo yayin da ake shirye-shiryen rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.

A majalisar dattawa, yan takara sun fara kokarin zawarcin yan majalisa don marawa kudirinsu na son darewa kujerar shugaban majalisar dattawan baya.

Masu neman takarar kujerar shugaban majalisar dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa: Yan Majalisa NA Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka - Rahoto Hoto: Orji Uzor Kalu, Godswill Obot Akpabio, Abdulaziz Yari
Asali: Facebook

Sanata Godswill Akpabio, Sanata Abdulaziz Yari da Sanata Orji Kalu duk suna takarar babbar kujerar.

Sai dai kuma, Akpabio shine zabin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) saboda goyon bayan da ya samu daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kwamitin aiki na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa: "Zaman Lafiyar Najeriya Ya Fi Aljihunmu Muhimmanci", Shettima Ga Sanatoci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da wadannan manyan goyon baya biyu da ya samu, har yanzu abubuwa sun dauki dumi a siyasar domin komai na iya faruwa, babban zaben 2023 na iya zama misali karara.

Ana ganin cewa yan takarar na iya amfani da karfin aljihunsu yayin da wanda ya saki bakin aljihu da kyau ka iya zama shugaban majalisar dattawa na gaba.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa kowani dan majalisa a zauren majalisar dattawan na iya siyar da kuri'unsa kan $5,000 da $10,000 ko ma fiye da haka."

Rahoton ya kuma tabbatar da cewar wasu zababbun sanatoci sun fara cinikin kuri'unsu da dukkanin yan takara da kuma yin ganawar sirri da manyan yan takarar kujerar shugaban majalisar dattawan.

Majiyar ta ce:

"Ban san ne ke faruwa a daya bangaren ba amma ina sane da cewar mutanen da ke ikirarin suna tare da mu sun sanyawa Yari hannu.

Kara karanta wannan

"Za Ka Koya Mun Yadda Ake Komawa Majalisa Ba Tare Da Zaben Fidda Gwani Ba", Okorocha Ya Yi Shagube Ga Lawan

"Ina bakin ciki cewa sanatoci na siyar da sa hannunsu kan tsakanin $5,000 da $10,000. Ba sa ma tambayar Yari abun da zai yi, kawai kudinsa suke so."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng