Kwankwaso Ya Yi Karin Haske Kan Tayin da Shugaba Tinubu Ya Masa Na Minista

Kwankwaso Ya Yi Karin Haske Kan Tayin da Shugaba Tinubu Ya Masa Na Minista

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni
  • Jim kaɗan bayan wannan zama, Kwankwaso ya ce sun ƙara magana kan kujerar Ministan da aka masa tayi a wannan gwamnati
  • Ya kuma maida martani ga zargin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce Abba Gida-Gida na kokarin cika alƙawarin kamfe ne a Kano

FCT Abuja - Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi karin haake kan tayin kujerar Minista a gwamnatin Tinubu.

Da yake jawabi ga 'yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Kwankwaso ya ce sun ƙara tattauna batun a wurin taron.

Kwankwaso da Tinubu.
Kwankwaso Ya Yi Karin Haske Kan Tayin da Shugaba Tinubu Ya Masa Na Minista Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Asali: Twitter

Kwankwaso ya ƙara da cewa a ganawar sun fi maida hankali kan batutuwan da suka danganci siyasa da shugabanci tare da shugaban ƙasa, wanda ya nuna gogewa da dabarun sanin makamar aiki.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Matakin da Shugaba Tinubu Ya Ɗauka Na Dakatar da Gwamnan CBN

A cewarsa yayin wannan zama batun naɗa shi a matsayin Minista a gwamnatin shugaba Tinubu ya ƙara tasowa, kuma ya tabbatar da cewa a shirye yake ya ba da gudummuwa wajen ci da Najeriya gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Daily Trust ya ce dangane da kujerar Minista kuma, tsohon gwamnan Kano ya ce:

"Mun kara tatttauna batun da shugaban ƙasa amma har yanzu bamu ƙarƙare ba, zamu ga yadda hakan zai haifar da ɗa mai ido, zamu yi farin ciki idan ƙasar mu ta matsa gaba."

Kwankwaso ya musanta zargin da Ganduje ya masa

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwa NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya musanta zargin da Abdullahi Ganduje ya masa cewa shi ya kulla manaƙisar rusau da ake a Kano.

Da yake martani ga kalaman Ganduje a Aso Rock bayan ganawa da shugaba Tinubu, Kwankwaso ya zargi magajinsa da suburbuɗa ƙarya, kamar yadda rahoton Vanguard ya tattaro.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu da Kwankwaso Sun Shiga Ganawa a Fadar Shugaban Kasa

Ya ce sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fara rusau ne domin cika alƙawarin da ya ɗaukarwa al'ummar Kano na kwato filaye da kadarorin gwamnati waɗanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta cefanar.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN

A wani rahoton na daban Shugaban Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Labarin muka samu yanzu haka ya nuna cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262