Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da ɗaya daga cikin yan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso
- Wannan ne karon farko da Tinubu ya shiga ganawa da Kwankwaso tun bayan hawa gadon mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023
- Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, yana cikin waɗanda suka gwabza da Bola Tinubu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023
FCT Abuja - Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa yanzu haka shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a Aso Rock, Abuja.
Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa na sahun gaba da suka kara da Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Tsohon gwamnan, wanda ya zo na huɗu a yawan kuri'u a sakamakon zaben da INEC ta ayyana, ya nemi zama kujera lamba ɗaya ne a inuwar New Nigeria People’s Party (NNPP).
"Ba Daina Zuwa Wurin Shugaba Tinubu Ba Saboda Abu 1" Gwamnan PDP da Yaje Villa Sau 4 a Sati Ya Faɗi Dalili
Legit.nga Hausa ta tattaro cewa Kwankwaso ne ɗan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci shugaba Tinubu a Aso Rock tun bayan kammala babban zaɓen 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan baku manta ba, a kwanakin baya rahotanni sun nuna cewa manyan 'yan siyasan biyu sun gana na tsawon awanni a birnin Faris na kasar Faransa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wannan ganawa ta yau Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023, ta kasance karo na biyu da Kwankwaso ya gana da Tinubu bayan na farko a watan da ya gabata ranar Litinin 25 ga watan Mayu.
Menene gaskuayar ganawar Kwankwaso da Tinubu a Faransa?
Wata majiya a cikin tawagar Kwankwaso ta tabbatar zaman taron a Faransa da cewa, "Eh tabbas sun gana da juna," inda ta ƙara da cewa amma a halin yanzu sun karkare tattaunawa.
Haka zalika wata majiya a tsagin Tinubu, ta shaida wa Channels tv cewa:
"Eh dagaske ne, sun gana a Faransa kamar yadda aka rahoto, wannan wata babbar alama ce dake nuna Tinubu yana nan a raye kuma da lafiya."
Shugaba Tinubu Ya Gana da Sarakuna
A wani labarin kuma Shugaba Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a Najeriya, Sultan ya yi jawabi mai jan hankali a wurin taron.
Ana tsammanin Tinubu zai taɓo batun haɗa kan kasa da kuma tsamo Najeriya daga yanayin da take ciki a zamansa da Sarakunan.
Asali: Legit.ng