Tinubu: Malamin Addini Ya Gargadi Shugaban Kasa Game Da Ba Wa El-Rufai Mukami, Ya Fadi Dalilansa
- Fitaccen malamin addinin Kiristanci ya gargaɗi Shugaba Bola Tinubu kan naɗa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, mamba a majalisar ministocinsa
- Fasto Primate Elijah Ayodele, ya ce dole ne shugaban ƙasa ya yi taka tsan-tsan da jigon jam’iyyar APC saboda kalaman da ya yi a kwanakin baya inda ake zarginsa da haɗa kai da Musulmin jiharsa
- Malamin ya kuma zargi El-Rufai da tafka maguɗi a zaɓen gwamnan Kaduna na 2023, tare da zarginsa da haddasa rikicin da ke faruwa a kudancin Kaduna
Primate Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya gargaɗi Bola Tinubu kan ya yi taka tsan-tsan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai saboda kalamansa kan Kiristocin jihar Kaduna, da kuma nuna goyon baya ga Musulmi.
Yana zargin El-Rufai da goyon bayan matakin bai wa Musulmai damar zabar wasu manyan muƙamai a jihar Kaduna, inda ya ƙara da cewa ya taka rawar gani wajen nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihar, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
Primate Ayodele ya kuma zargi El-Rufai da kitsa batun tikitin Musulmi da Musulmi na APC
Da yake gabatar da tsokaci, malamin ya bayyana cewa kalaman da tsohon gwamnan ya yi, ka iya jefa ƙasar nan cikin rikicin addini idan ba a taka masa burki ba, kamar yadda PM News ta wallafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malamin addinin ya kuma zargi El-Rufai da zama ummul aba'isin tikitin Musulmi da Musulmi na APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, haka nan kuma ya zargeshi da haddasa rikicin addini a Kudancin Kaduna.
Daga nan sai Ayodele ya gargaɗi shugaba Tinubu, a kan kar ya kuskura ya bai wa El-Rufai kowane irin muƙami a gwamnatinsa domin kaucewa rugujewar Najeriya.
Primate Ayodele ya faɗawa Tinubu cewa El-Rufai ba abin yarda ba ne
Faston ya shawarci Shugaba Tinubu kan cewa kar ya amince da El-Rufai, saboda yana zarginsa da tafka maguɗi a zaɓen gwamnan jihar Kaduna, da ɗan takarar APC ya yi nasara.
Ya ƙara da cewa Ubangiji zai ƙwace kujerar gwamnan da ya ce an samu ta hanyar maguɗi, ya miƙata zuwa hannun mai ita.
Idan za a iya tunawa, El-Rufai ya kasance babban jigo a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar CAN ta soki El-Rufai kan kalaman da ya yi
Legit.ng ta kawo muku cewa Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna, ta caccaki tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai, bisa kalamansa kan batun tikitin Musulmi da Musulmi.
Shugaban kungiyar na jihar Kaduna, John Joseph Hayab ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng