Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Gwamnonin Jihohin Plateau Da Akwa Ibom
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin Plateau da Akwai Ibom a Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja
- Ganawar shugaban ƙasar da gwamnonin biyu na zuwa ne bayan ya yi taro da gwamnonin Najeriya ranar Laraba
- Shugaban ƙasar zai kuma sake sanya labule da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah a fadar shugaban ƙasan bayan kammala ganawa da gwamnonin biyu
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang da takwaransa na jihar Akwa Ibom, Umo Eno, a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ganawar ta su ta fara ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Alhamis, 8 ga wataɓ Yunin 2023.
Zaman na su na zuwa ne bayan shugaba Bola Tinubu ya gana da ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Laraba, inda ya buƙaci gwamnonin da su bayar haɗin kai su yi aiki tare da gwamnatin tarayya.
Gwamnan jihar Akwa Ibo, Umo Eno bai samu halartar taron na ranar Laraba da shugaba Tinubu ya yi da gwamnonin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da cewa gwamnonin tare suka nufi ofishin shugaban ƙasar, babu tabbacin sun yi ganawar ne a tare ko daban-daban, cewar rahoton Vanguard.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa shugaban ƙasar zai sanya labule da gwamnan jihar Enugu, bayan ya kammala ganawa da gwamnonin na jihohin Plateau da Akwa Ibom.
Tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki, ya gudanar da tarurruka da dama da masu ruwa da tsaki a ɓangarori da dama na ƙasar nan, domin sanin inda zai dosa a mulki.
Akpabio Ne Zaben Tinubu a Shugabancin Majalisa
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa zaɓaɓɓen sanara daga jihar Borno, Sanata Ali Ndume, ya bayyana zaɓin shugaba Bola Tinubu akan shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya gaya masa cewa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, shine zaɓinsa a kujerar shugabancin majalisar dattawa.
Sanata Ndume yana daga cikin na gaba-gaba wajen ganin Sanata Akpabio ya ɗare shugabancin majalisar.
Asali: Legit.ng