Magoya Bayan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC a Jihar Ƙogi
- Jam'iyyar PDP ta rasa wasu manyan jiga-jiganta a yankin ƙaramar hukumar Kabba/Bunu, jihar Kogi
- Magoya bayan PDP sun tattara kayansu sun koma APC mai mulki kuma sun samu kyakkyawar tarba daga gwamna Yahaya Bello
- A cewar jagoran tawagar, shugabancin Bello da wasu ɗabi'un da ya nuna ne suka ja hankalinsu zuwa APC
Kogi State - Jiga-jigai kuma tsofaffin shugabannin jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Kabba/Bunu, jihar Kogi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
The Nation ta rahoto cewa gwamna Yahaya Bello ne ya karbi masu sauya shekar a gidan gwamnatinsa da ke Lokoja, babban birnin jihar ranar Talata, 5 ga watan Yuni.
Gwamna Bello ya yi alkawarin tabbatar da ba'a nuna banbanci ko wariya a tsakanin tsaffi da sabbin mambobin jam'iyyar APC ba.
Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau
Ya kuma bukaci yan siyasan tsagin adawa su zubar da makamai, su rungumi APC domin ba da gudummuwa a kokarin gwamnatinsa na inganta walwala da jin daɗin mazauna Kogi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bello ya bayyana cewa jami'ar jiha da ya kirkira a Okunland, zata ɗauki rukunin ɗalibanta na farko gabannin ƙarewar wa'adin mulkinsa.
Meyasa jiga-jigan suka yanke shawarin koma wa APC?
Da yake jawabi a madadin masu sauya shekar, tsohon ɗan majalisa kuma tsohon ma'ajiyin PDP a Kabba/Bunu, Alfred Bello, ya yaba wa gwamna Belli bisa masarar da ya samu ɓangaren zuba ayyukan ci gaba.
Ya ce:
"Shugabancin mai girma gwamna abin koyi ne domin tattare yake da jawo kowa a jiki, adalci da daidaito, waɗan nan suna cikin dalilan da suka ja hankalinmu muka shiga APC."
Haka zalika ya yaba wa gwamna Bello bisa yunƙurin kafa jami'a mallakin jihar Kogi a Okunland, inda ya jaddada cewa ilimin gaba sakandire ya yi ƙaranci a yankin.
Tsohon jigon PDP ya tabbatarwa gwamnan cewa zasu yi aiki ba dare ba rana domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben gwamnan jihar mai zuwa a watan Nuwamba.
Majalisar dokokin Kogi ta yi sabon shugaba da mataimaki
A wani rahoton kuma kun ji cewa mambobi sun zaɓi sabon kakakin majalisar dokokin jihar Kogi da mataimakinsa.
Yusuf Umar daga mazaɓar Lokoja II ne ya samu nasarar zama kakakin majalisa bayan mambobi sun kaɗa masa kuri'u ba adawa.
Asali: Legit.ng