Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ta Rantsar da Yusuf Umar a Matsayin Sabon Kakaki

Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ta Rantsar da Yusuf Umar a Matsayin Sabon Kakaki

  • Majalisar dokokin jihar Kogi ta zabi sabon kakaki da mataimakinsa bayan gwamna Yahaya Bello ya rantsar da ita ranar Talata
  • Yusuf Umar daga mazaɓar Lokoja II ne ya samu nasarar zama kakakin majalisa bayan mambobi sun kaɗa masa kuri'u ba adawa
  • Haka nan sun zabi Honorabul Paul Enema a matsayin mataimakin kakakin majalisar kuma nan take suka karbi rantsuwar kama aiki

Kogi - Alhaji Yusuf Aliyu Umar, mai wakiltar mazaɓar Lokoja II, ya samu nasarar zama kakakin majalisar dokokin jihar Kogi ranar Talata bayan mambobi sun zabe shi da harshe ɗaya.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Honorabul Rin Ebama-Shehu, mai wakiltar mazaɓar Lokoja I ne ya gabatar za Umar a matsayin wanda ya dace da kujerar kakakin.

Yusuf Umar.
Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ta Rantsar da Yusuf Umar a Matsayin Sabon Kakaki Hoto: thenation
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa nan take Honorabul Suleiman Abdulrasaq, na mazabar Okene 1, ya goyi baya kuma baki ɗaya 'yan majalisar suka biyo baya suka kaɗa masa kuri'unsu.

Kara karanta wannan

Mai Shekara 38 Ya Zama Shugaba Yayin da Aka Rantsar da Sababbin ‘Yan Majalisa

Haka nan kuma majalisar ta zaɓi Honorabul Paul Enema, mai wakiltar mazaɓar Dekina/Okura a matsayin mataimakin kakakin majalisa dokokin Kogi ta 8.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar da Enema sun amince da naɗin da kuma zaɓensu a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa, kamar yadda rahoto ya tabbatar.

Majalisa ta rantsar da sabbin shugabannin nan take

Daga nan sai magatakardan majalisar ya jagoranci rantsuwar kama aikin sabbin shugabannin da aka zaɓa a majalisa ta 8 da zangonta ya fara daga ranar Talata.

Da yake jawabi, sabon kakakin majalisar ya miƙa dukkan godiya ga Allah kana ya gode wa sauran abokan aikinsa yan majalisu bisa ganin ya dace ya ba da gudummuwarsa a wannan matsayi.

Umar ya sha alwashin cewa zai jagoranci majalisar dokoki tare da sauran ɓangarorin gwamnati wajen bunkasa jihar Kogi ta kai matsayi mafi kololuwa.

Tun a farkon zaman, magatakardan majalisa ya karanta wasiƙar gwamna Yahaya Bello, inda ya shelanta rushe tsohuwar majalisa da kafa sabuwa kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Rantsar da Majalisar Dokoki Ta 7, An Zabi Sabon Kakakin Majalisa da Mataimaki

Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa

A wani rahoton na daban kuma Majalisar dokokin jihar Ekiti ta zabi sabon kakakin majalisa, mataimaki da sauran manyan muƙamai.

Mambobin majalisar sun amince da zaɓen Honorabul Adeoye Aribasoye a matsayin sabon kakakin majalisa ta 7 da Bolaji Olagbaju a matsayin mataimaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262