Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa

Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa

  • Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya shelanta rantsuwar kama aikin majalisar dokokin jihar ranar Talata, 6 ga watan Yuni
  • Mambobin majalisar sun amince da zaɓen Honorabul Adeoye Aribasoye a matsayin sabon kakakin majalisa ta 7
  • Bayan haka yan majalisar sun zabi mataimakin kakaki, shugaban masu rinjaye, shugaban marasa rinjaye da sauran muƙamai

Ekiti - Tsohon shugaban kwamitin midiya da harkokin hulɗa za jama'a na majalisar dokokin jihar Ekiti, Adeoye Aribasoye, ya samu nasarar zama sabon kakaki majalisar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa Honorabul Aribasoye, mai wakiltar mazaɓar Ikole karkashin inuwar APC, ya zama kakakin majalisar ba tare da jayayya ba ranar Talata.

Adeoye Aribasoye.
Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa Hoto: punchng
Asali: UGC

Aribasoye, tsohon mai ladabtarwa a majalisar dokokin wacce aka rushe, ya samu nasarar zama shugaba bayan gwamna Biodun Oyebanji, ya rantsar da sabuwar majalisa ta 7 mai mambobi 26.

Kara karanta wannan

Mai Shekara 38 Ya Zama Shugaba Yayin da Aka Rantsar da Sababbin ‘Yan Majalisa

Bayan haka Bolaji Olagbaju na jam'iyyar APC mai wakiltar mazaɓar Ado Ekiti II ya samu nasarar zama mataimakin kakakin majalisar ba tare da hamayya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran shugabannin da aka zaɓa a a majalisar sun haɗa da, shugaban masu rinjaye, Tolulope Ige (APC, Ekiti ta kudu maso yamma II); da shugaban marasa rinjaye, Dele Ogunsakin na SDP.

Na shirya wannan aikin da ya hau kaina - sabon Kakaki

Da yake jawabi bayan samun nasara, Aribasoye ya ce:

"Na shirya tsaf don ɗaukar nauyin da aka ɗora mun, duk da ba abu ne mai sauki ba amma zamu iya ɗauka. Mun shirya yin dokokin da zasu kawo ci gaba a jiharmu, dokokin da zasu yi tasiri a rayuwar mazauna jihar Ekiti."

Sabon shugaban majalisar ya ce majalisa ta 7 ta shirya aiki kafaɗa da kafaɗa da bangaren zartarwa domin tabbbatar da cewa mutanen Ekiti sun sha romom demokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mambobi Majalisa Sun Zabi Kakakin Majalisar Dokoki Jihar APC Karo Na 3 a Jere

AIT TV ta rahoton sabon kakakin na cewa:

"Mun shirya haɗa hannun da dukkan masu ruwa da tsaki na jihar Ekiti domin bunƙasa jiharmu zuwa matakin da muke fata."

Obasa Ya Sake Samun Nasarar Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas

A wani labarin kuma mambobi majalisa sun zabi kakakin majalisar dokoki jihar Legas karo na 3 a jere.

Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Agege 01, Dakta Mudashiru Ajayi Obasa, ya sake lashe zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Legas ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262