Uwar Gidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, Ta Shiga Ofis, Ta Fara Aiki
- Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fara shiga ofishin 'First Lady' jiya Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023
- Misis Tinubu, ta ziyarci manyan ofisoshin sashinta domin ganin yadda komai ke tafiya tare da babban sakataren gidan gwamnati
- A ranar 29 ga watan Mayu, aka rantsar da mijinta, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya
FCT Abuja - Uwar gidan shugaban ƙasa "First Lady," Sanata Oluremi Tinubu, ta shiga ofishinta domin fara aiki a matsayin mace lamba ɗaya a Najeriya ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Misis Tinubu ta isa bangaren matar shugaban ƙasa bisa rakiyar masu tsaronta a Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Facebook
Daga zuwanta, ta samu kyakkyawar tarba daga babban Sakataren fadar shugaban ƙasa, Mista Tijjani Umar, da shugabannin ɓangarorin sashin matar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba
Wane aiki matar shugaba Tinubu ta fara yi a ranar farko?
Daga nan, matar shugaban ƙasa ta fara tafiya rangadi domin duba ofishin da ke ɓangarenta, wanda ya haɗa da ofishin shugabanci, ICT, shirye-shirye, midiya da kuma ofishin tsara ayyuka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An haifi Oluremi Tinubu a ranar 21 ga watan Satumba, 1960, mahaifiyarta yar kabilar Itsekiri ce yayin da mahaifinta ya kasance bayerabe.
Ta yi aiki a matsayin matar gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007, daga nan kuma ta lashe zaɓen Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.
Sanata Oluremi Tinubu ta shiga harkokin taimako da ba da tallafi da dama da nufin sanya walwala da jin daɗi a fuskokin mutane masu ƙaramin karfi a mazaɓarta.
Ta taɓa haɗa gasar karanto haruffan kalma da aka fi sani da, "Spelling Bee competition," a tsakanin daliban sakandiren jihar Legas wanda ya samar da gwamnan rana ɗaya a zangon mulkin mijinta.

Kara karanta wannan
Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani
Mai gidanta, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar lashe zaben shugaban ƙasa wanda ya gudana a watan Fabrairu kuma aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa
A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsoffin gwamnoni 3 a fadarsa da ke birnin Abuja.
Rahoto ya nuna tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Ebonyi, Dave Umahi da Godswill Akpabio sun isa Villa da karfe 2:33 na ranar Litinin.
Asali: Legit.ng