Jerin Manyan Fastocin Da Suka Kyale Coci Suka Zama Gwamnoni a Jihohinsu

Jerin Manyan Fastocin Da Suka Kyale Coci Suka Zama Gwamnoni a Jihohinsu

Ba kasafai ake samun malaman addini musamman fastoci, a cikin harkokin siyasa ba. Hakan ya sanya wasu cocikan basu yarda fastocinsu su shiga siyasa.

Sai dai, wasu fastoci ƴan kaɗan sun kauce wannan layin inda suka tsunduma cikin harkokin siyasa, inda har wasu daga cikinsu suka zama gwamnonin jihohinsu.

Jerin fastocin da suka zama gwamnoni a jihohinsu
Manyan fastocin da suka zama gwamnoni a jihohinsu Hoto: Rev Fr Hyacinth Alia/Rev T Nyame/Umo Uno
Asali: Facebook

Legit.ng ta yi duba kan waɗannan fastocin da suka yi samu nasarar zama gwamnoni bayan sun shiga siyasa.

Rev. Fr. Moses Orshio Adasu

Na farko a cikin jerin shi ne Rev. Fr. Moses Orshio Adasu, wanda ya yi suna bisa furucin da ya yi na cewa siyasa ba mugun wasa bane amma waɗanda ke yin ta domin son zuciya sune suka mayar da ita mugun wasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

"Na Koyi Darasi": Matashi Ya Ajiye Aikinsa Mai Gwabi Domin Ya Kasance Da Budurwarsa, Sun Rabu Bayan Sati 2

"Na shiga siyasa ne domin in tsarkaketa ta koma mai tsafta." A cewarsa.

Faston wanda ya rikiɗe ya koma ɗan siyasa ya zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar Benue na biyu bayan an gudanar da zaɓe a ranar 2 ga watan Janairun 1992, inda ya lashe zaɓen a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Sai dai, bai daɗe akan mulki ba saboda juyin mulkin da Janar Sani Abacha ya yi a watan Nuwamban 1993, inda aka maye gurbinsa da Kyaftin Joshua Obademi.

Jolly Nyame

Jolly Tavoro Nyame, wanda aka haifa a ranar 25 ga watan Disamban 1955, babban fasto ne a cocin United Methodist Church of Nigeria. An zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar Taraba a shekarar 1992 bayan ya shiga siyasa.

Sai dai, shi ma kamar Agasu bai daɗe kan mulki ba saboda juyin mulkin Janar Sani Abacha.

Nyame ya sake komawa siyasa inda aka zaɓe shi gwamnan jihar Taraba a shekarar 1999, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar People's Democratic Party (PDP), sannan ya sake komawa a karo na biyu a shekarar 2003.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2003, ta sanya ya zama shi kaɗai ne aka taɓa zaɓa har sau uku a matsayin gwamnan jihar Taraba.

Rabaran Hyacinth Alia

Rev Fr Hyacinth Iormem Alia ya fusata cocin Katolika inda aka dakatar da shi a watan Mayun 2022, bayan ya bayyana aniyarsa ta neman tikitin takarar gwamnan jihar Benue a ƙarƙashin inuwar All Progressives Congress (APC).

Alia, wanda ya ke tare da cocin Katolika ta Gboko, ya zama ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC inda daga baya ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Hyacinth ya zama fasto na biyu da ya taɓa zaman gwamnan jihar Benue bayan Adasu.

Fasto Umo Eno

Fasto Umo Eno shi ne ya kafa cocin All Nations Christian Ministry International a jihar Akwa Ibom. Uno ya yi takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, a zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Eno ya lashe zaɓen gwamnan jihar ne bayan ya samu ƙuri'u 354,348 inda ya lallasa Akanimo Udofia na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 129,602 da ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Uduakobong Udoh wanda ya samu ƙuri'u 4,746.

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tsallake ƙalubale da dama kafin ya samu ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan.

Shugaban ya tsallake rijiya da baya sosai kafin ya hau kan madafun ikon ƙasar nan, bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya kammala wa'adin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng