“Gaba Daya Gwamnoni 13 a Shirye Suke Su Taka Rawar Gani”: Makinde Ga Atiku Da Shugabannin PDP

“Gaba Daya Gwamnoni 13 a Shirye Suke Su Taka Rawar Gani”: Makinde Ga Atiku Da Shugabannin PDP

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, ya gana da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, bayan fafatawar da suka yi a zaben da aka kammala
  • Atiku ya kuma gana da magajin tsohon gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Siminalayi Fubara a wajen taron PDP da aka yi a jihar Bauchi a ranar Lahadi
  • A jawabinsa wajen taron, Makinde ya nuna shirin gwamnonin PDP na bayar da hadin kai wajen farfado da jam'iyyar da kuma aiki saboda gaba

Bauchi - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara gyara hargitsin da ta shiga a siyasar Najeriya yayin da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu gwamnonin jam'iyyar, ciki harda fusatattun 'ya'yan jam'iyyar suka gana.

Atiku da zababbun jami'an jam'iyyar, ciki harda Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas sun halarci taron da aka shirya ma zababbun jami'an PDP, inda Gwamna Bala Mohammed na jihar Buachi ma ya hallara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jihar Bauchi Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar PDP

Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP
“Gaba Daya Gwamnoni 13 a Shirye Suke Su Taka Rawar Gani”: Makinde Ga Atiku Da Shugabannin PDP Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

PDP ta sake yunkuri a karo na biyu don shirya Atiku, Makinde, Wike da sauran shugabannin PDP

Taron shine irinsa na biyu da jam'iyyar ke yi don yin sulhu tsakanin fusatattun gwamnoninta da shugabancin jam'iyyar tun bayan babban zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin rikice-rikicen da ya dabaibaye PDP gabannin babban zaben 2023 shine kafa gwamnonin G5 karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kuma Makinde wanda ya kasance babban dan kungiyar ya halarci taron.

Da ya je shafinsa na Twitter a yammacin ranar Lahadi, 3 ga watan Yuni, Makinde ya ce ya bayyana a taron cewa ya kamata a magance matsalolin da ke cikin jam'iyyar sannan a fara warkewa daga illa da hakan ya yi.

Makinde ya sanar da Atiku da sauran shugabannin PDP shirinsu na rungumar zaman lafiya

Da yake magana a madadin gwamnonin jam'iyyar, Makinde ya ce gwamnonin 13 a shirye suke su taka rawar gani don daidaita jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Muhimman Abubuwan da Su Wike Suka Tattauna da Shugaba Tinubu a Aso Rock Sun Bayyana

Ya ce:

"A madadin gwamnonin PDP, na bayyana cewa dukkanin gwamnoni 13 a shirye suke su taka rawar gani a jam'iyyarmu."

Ga wallafarsa a kasa:

Kujerar dan majalisar tarayya: Al Makura ya janye karar da ya shigar kotun zabe

A wani labarin kuma, mun ji cewa Sanata Umaru Tanko Almakura ya janye karar da ya shigar kotun zabe.

Tsohon gwamnan ya kalubalanci sakamakon zaben sanatan Nasarawa ta kudu wanda PDP ta yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng