An Tsaida Ranar da Tinubu Zai Zauna da Sanatoci, ‘Yan Majalisar Jam’iyyun Adawa
- Bola Ahmed Tinubu ya aika goron gayyata ga zababbun Sanatocin da ‘yan majalisar wakilan tarayya
- Sabon shugaban Najeriyan zai kebe da sababbin Sanatoci, daga nan sai ya hadu da zababbun ‘yan majalisa
- Zaman da za ayi a Aso Rock zai ba ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayyar damar haduwa da Shugaban kasar na su
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai zauna da zababbun Sanatocin da ‘yan majalisar wakilan tarayya da ke karkashin jam’iyyun hamayya.
Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa a ranar Litinin mai zuwa, sabon shugaban Najeriya zai gana da ‘yan adawan da za a rantsar a majalisun tarayya.
Ana kyautata zaton cewa zaman bai rasa nasaba da kokarin Bola Ahmed Tinubu na ganin gwamnatinsa ta samu kyakkyawar alaka da ‘yan majalisa.
Gayyatar da aka aikawa zababbun Sanatoci ya nuna Tinubu zai hadu da su da karfe 3:00 na ranar Litinin, sai ya hadu ‘yan majalisar wakilai da karfe 5:00.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar Tijjani Umar
Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar ya aika da goron gayyatar a madadin shugaban ma’aikatan fada, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.
Rahoton ya ce Umar ya bukaci ‘yan majalisar su gabatar da sunayensu domin jami’an tsaro su iya tantance su wajen shiga fadar Aso Rock Villa da yake Abuja.
Tinubu ya hadu da Lawan
Zaman zai zo kwanaki kadan kenan bayan Tinubu ya hadu da shugabannin majalisa masu barin-gado da ‘yan takaran da jam’iyyarsa ta tsaida a zaben bana.
Baya ga APC mai mulki da rinjaye a majalisa, jam’iyyun siyasa na PDP, LP, NNPP, SDP da YPP duk su na da wakilci a majalisar da za a rantsar a watan nan.
Duk da rinjayen APC a majalisun dattawa da ta wakilai, jam’iyyar sai ta hada-kai da sauran ‘yan adawa domin ta samu goyon baya da kyau a mulkinta.
A zaben majalisar dattawa, APC ta tsaida Godswill Akpabio da Jubrin Barau a matsayin ‘yan takaranta domin gudun kuskuren da aka yi a Yunin 2015.
Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu su ne ‘yan takaran jam’iyya mai-ci a zaben majalisar wakilai.
Takarar Abdulaziz Yari
Rahoto ya zo cewa Abdulaziz Yari ya ziyarci Shugabannin NNPP, kuma ya nuna zai gana da Jam'iyyun PDP, APGA LP, SDP da YPP a game da takararsa.
Zababben Sanatan ya hada-kai da Orji Uzor Kalu, Sani Musa da Osita Izunaso domin a karya APC. Yari ya na ganin bai dace a bar kujerar ta tafi Kudu ba.
Asali: Legit.ng