Gwamna Bala Mohammed Ya Zama Sabom Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
- Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zaɓi sabon shugaba wanda zai shugabance ta
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin na jam'iyyar adawa ta PDP
- Gwamnan ya nun godiyarsa kan wannan matsayi da aka ba shi inda ya buƙaci takwarorinsa da su ba shi dukkan haɗin kan da ya kamata
Jihar Bauchi - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnoninta.
Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, shine ya bayyana hakan bayan gwamnonin jam'iyyar sun kammala sa labulen da suka yi a ofishin gwamnan jihar Bauchi ranar Asabar, cewar ahoton Punch.
Gwamnonin jam'iyyar PDP, mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na ƙasa, da ƙusoshin jami'iyyar sun taru a babban ɗaƙin taro na fadar gwamnatin jihar Bauchi, domin yi wa waɗanda suka lashe zabe ƴan jam'iyyar maraba.
Da ya ke gabatar da sanarwar, gwamna Fintiri ya bayyana cewa gwamɓa Bala Mohammed, zai maye gurbin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, inda ya ƙara da cewa an kuma zaɓi gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a matsayin mataimakin shugaba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Cancantar gwamna Bala Mohammed ta sanya ya samu shugabancin ƙungiyar
Ya bayyana cewa an zaɓi gwamnan na jihar Bauchi ne a matsayin shugaban ƙungiyar saboda cancantarsa da ƙwarewar da ya ke da ita domin ƙara farfaɗo da ƙungiyar, jaridar Vanguard ta yi rahoto.
Da ya ke jawabinsa, gwamna Bala Mohammed, ya bayyana wannan sabon matsayin da ya samu a matsayin abu mai daraja a wajensa da dukkanin mutanen jihar Bauchi, sannan ya buƙaci sauran takwarorinsa da su mara masa baya domin ciyar da ƙungiyar gaba.
Gwamnan Taraba Ya Shirya Bincikar Magabacinsa
A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Agbu Kefas, ya shirya gudanar da bincike kan gwamnatin da ya gada ta gwamna Darius Ishaku.
Gwamna Kefas ya bayyana cewa zai bi diddigin yadda gwamnatin magabacinsa ta tafiyar da harkokin kuɗaɗen jihar, inda ya da cewa wajen da ya lura akwai alamar tambaya dole ya yi tambaya akai.
Asali: Legit.ng