Matawalle Ya Siyo Motocin N2.79bn Amma Bai Bar Ko Daya Ba, Gwamnan Zamfara
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya zargi magabacinsa da sace motocin gwamnati da suka kai na biliyan N2.79bn
- Sabon gwamnan ya bayyana yadda gwamnatin Matawalle ta ware kudaɗe daban-daban ta siyo motocin a lokacin mulkinta
- Ya kuma baiwa tawagar tsohon gwamnan wa'adin kwanakin aiki 5 su dawo da motocin cikin ruwan sanyi
Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce wanda ya gabace shi, Bello Matawalle, ya ware kuɗin gwamnati kimanin biliyan N2,794,337,500 ya siyo motoci.
Amma a cewar sabon gwamnan, Matawalle bai bar ko ɗaya daga cikin motocin ba sa'ilin da ya sauka daga kan karagar mulkin Zamfara ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.
Kakakin gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Gwamnan ya ce Matawalle ya ba da kwangilar siyo motocin da za'a raba wa manyan jami'an gwamnati a ma'aikatu, sashi-sahi da hukumomin na kimanin N1,149,800,000.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, a wancan lokacin gwamnatin Zamfara karkashin Matawalle ta bai wa kamfanin Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD kwangilar cefano motocin.
Matawalle ya sake fitar da wasu kuɗin
Lawal ya kuma zargin cewa Matawalle ya kashe N484,512,500 wajen sayo motocin sulƙe Jeep guda uku, N459,995,000 na cefano Prado Jeep guda bakwai da Land Cruiser ɗaya, sai kuma N228,830,000 domin sayo Toyota Hilux 7.
Gwamnan ya ƙara da cewa an ƙara ware wasu N130,000,000 wajen siyo motocin Peugeot 406 guda 30 da motar Land Cruiser ɗaya, da kuma N160,000,000.00 da aka sayo Land Cruiser Jeep guda biyu.
Duk bayan wannan, gwamnatin Matawalle ta ƙara ware N120,000,000 domin karɓo Motocin ofishin mataimakin gwamna.
Sanarwan ta ce:
"Wannan babban zubda mutunci ne ga APC a ce duk waɗan nan motocin da aka siyo da aljihun gwamnati gwamna mai barin gado da muƙarrabansa sun yi awon gaba da su."
"Mun tuntuɓi tsohon gwamna Bello Matawalle a hukumance kuma mun ba shi wa'adin kwanakiin aiki 5 ya dawo da motocin nan cikin ruwan sanyi."
Bani da Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa Jam'iyar APC, Wike
A wani labarin kuma Tsohon gwamnan PDP, Nyesom Wike ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin tattara kayansa ya koma APC mai mulki.
Wike, jigon jam'iyyar PDP kuma jagoran tawagar G-5, ya ce sun gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne don jaddada goyon baya.
Asali: Legit.ng