Faɗa da Cikawa: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Fara Rusau a Birnin Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya fara aikin rusau kamar yadda ya yi alkawari a jihar Kano
- Kwamitin da ya kafa kuma ya ɗora wa aiki ya fara rushe wasu gine-gine da filin Sukuwar Dawaki da daren ranar Jumu'a
- Tun a wurin rantsuwar kama aiki, Abba Gida-Gida ya umarci hukumomin tsaro su kwace iko da wuraren da aka cefanar ba kan ƙa'ida ba
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Ƙabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya fara aikin rushe gine-ginen da ake zargin filayen gwamnati ne da aka siyar ba kan ƙa'ida ba.
Daily Trust ta rahoto cewa da daren ranar Jumu'a kwamitin da gwamna ya kafa kan lamarin, ya fara rushe gine-gine a Filin Sukuwa da ke cikin birnin Kano.
Idan baku manta ba, a jawabinsa na wurin rantsuwar kama aiki, Abba Gida-Gida ya umarci hukumomin tsaro su kwace iko da duk wasu kadarori da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta cefanar.
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A yau, ina sanar muku da cewa dukkan filaye da kadarori waɗanda gwamnatin Ganduje ta bi ta bayan fage ta sayar zamu kwato su, hukumomin tsaro tun daga yan sanda, DSS, Sibil Defens da Hisbah su karɓe wurin kafin mu yanke hukunci."
Wasu daga cikin kadarorin da gwamna Abba ke nufi sun haɗa da filayen makarantu, filayen idi da kuma wuraren da ake gudanar da bukukuwan Al'ada a cikin Kano.
Sauran sun ƙunshi, filayen Asibitoci manya da kanana, maƙabartu da sauran wuraren daban-daban a cikin birni da kewayen jihar Kano, waɗanda tsohon gwamna ya cefanar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa zata kafa hukumar binciken shari'a nan gaba domin, "tabbatar da duk mai hannu da wanda ya taimaka wajen cefanar da kadarorin sun girbi abinda suka shuka."
Gwamnonin PGF Sun Ɗauki Matsaya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya
A wani labarin kuma Gwamnonin APC sun gana da shugaba Tinubu, sun goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya yi Alla-wadai da ƙara farashin a tsohon kaya.
Asali: Legit.ng