Zababben Sanata Zai Birkita APC, Ya Jawo Tinubu Ya Zauna da Shugabannin Majalisa

Zababben Sanata Zai Birkita APC, Ya Jawo Tinubu Ya Zauna da Shugabannin Majalisa

  • Abdulaziz Yari ya hada-kai da wasu Sanatoci da ‘Yan Jam’iyyun adawa a zaben majalisar dattawa
  • Tsohon Gwamnan ya tsaya takarar shugabancin majalisa, da alama zai yaki wadanda APC ta tsaida
  • Yari ya na ziyartar jam’iyyun adawa, ya nuna kundin tsarin mulki bai hana masa tsayawa takara ba

Zamfara - Daya daga cikin manyan masu neman takara a majalisa, Abdul’aziz Yari ya na neman yin fito na fito da jam’iyyarsa ta APC mai mulki.

A rahoton da aka samu daga Tribune, an fahimci Abdul’aziz Yari wanda zai wakilci Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, ya dage a kan takararsa.

Tsohon Gwamnan ya na yakar jam’iyyarsa ta APC da ta ayyana Godswill Akpabio da Jibrin Barau a matsayin ‘yan takararta a zaben majalisar dattawa.

Abdulaziz Yari
Abdulaziz Yari tare da Shugabannin NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A ranar Alhamis, Yari ya ziyaci sakatariyar jam’iyyar NNPP da ke garin Abuja, bisa dukkan alamu ya na neman karin goyon bayan ‘yan adawa a zaben.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa: Tsoffin Sanatocin APC Sun Bukaci Kalu, Yari Da Sauransu Su Janye Daga Tseren Kujerar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NNPP ta karbi Yari

Da yake jawabi a babban ofishin na NNPP, Alhaji Yari ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasa ya sa a gaba a neman shugabancin majalisar tarayya.

‘Dan siyasar ya soki masu amfani da addini wajen kushe ‘yan takaran da ya ce sun cancanta.

Yari ya tabbatar da cewa ba zai hakura da neman kujerar nan ba, kuma zai cigaba da ganawa da masu ruwa da tsaki domin ganin hakarsa ta cin ma ruwa.

Saura Jam'iyyun LP, SDP dsr

Nan ba da dadewa ba, za a ga sabon Sanatan a ofishin jam’iyyun hamayya na APGA, SDP, LP, PDP da kuma wanda duk su na da kujeru a majalisar dattawa.

Zababben Sanatan ya tunawa mutane lokacin da David Mark and Ike Ekweremadu su ka taba rike majalisar dattawa, alhali dukkansu biyun kiristoci ne.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Wadanda ke jirgin Yari

The Cable ta ce Yari ya fadi sauran Sanatocin da suke tare da shi a takarar nan da ya sa gaba, daga ciki har da wanda ya karyata zancen hadin-kan na su.

"Mu na aiki tare Orji Uzor (Kalu), (Sani) Musa da kuma (Osita) Izunaso da ni karon kai na. Za mu cigaba da yin wannan gwagwarmaya tare.
Ba a san ma ci tuwo ba, sai miya ta kare. Abin kwarin gwiwar shi ne jawabin shugaban kasa da ya ce zai bi tsarin mulki wajen shugabanci."

APC ta zauna da masu takara

A baya an samu rahoto cewa wasu wadanda suke neman kujerar Ahmad Lawan sun nuna za su yi fito na fito da jam’iyyarsu ta APC a zaben majalisar.

Shugaban Jam’iyyar APC ya zauna da Orji Kalu, Sani Musa, da Abdulaziz Yari domin ya lallashe su, amma da alama wasunsu ba su fasa neman mulki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng