Wike, Ganduje, Ribadu Da Wasu Yan Siyasa Da Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministoci

Wike, Ganduje, Ribadu Da Wasu Yan Siyasa Da Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministoci

  • Rahotanni sun kawo cewa shhugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tattara kan majalisarsa da tawagar tattalin arziki kafin rantsarwa a ranar 29 ga watan Mayu
  • Wata majiya ta bayyana cewa Tinubu ya mayar da hankali wajen kafa tawagar kwararru domin aiwatar da ajandarsa da cika manyan burukan yan Najeriya
  • Yayin da aka fi so a zabi yan APC, wasu kwararrun mutanen daga wajen jam'iyyar ma na iya samun manyan mukamai a gwamnatin

Wani rahoton jaridar Nigerian Tribune ya nuna cewa ta yiwu Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya fara kafa majalisarsa da tawagar masu kula da ragamar tattalin arziki.

An rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Bola Tinubu da manyan yan siyasa
Wike, Ganduje, Ribadu Da Wasu Yan Siyasa Da Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministoci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike, Femi Gbajabiamila, Aisha Binani
Asali: Facebook

A wani rahoto da ta bayyana a ranar Laraba, 17 ga watan Mayu, jaridar ta nakalto wata majiya tana cewa shugaban kasar ya mayar da hankali wajen aiki ya kuma jajirce wajen hada kwararrun mutane da za su taimaka masa wajen cimma sabuwar ajandarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu Bai Nada Gbajabiamila a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fada ba - Hadiminsa

An nakalto majiyar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zababben shugaban kasar ua san cewa mutane suna sa rai kan abubuwa da yawa kuma yana sane da rashin hakurin yan Najeriya. Baya son bata rawansa da tsalle, don haka yana son shirya tawagarsa zuwa 29 ga watan Mayu."

A cewar majiyar da ba a bayyana sunanta ba, ga jerin manyan yan siyasar da ake ganin Tinubu zai ba mukamai da kuma mukaman da za su iya samu a majalisarsa.

Jan Hankali: Wadannan sunaye/mukamai da aka jero a kasa wata majiya da Nigerian Tribune ta nakalto ne ya fada kuma bai fito daga shafukan shugaban kasar ba.

S/NSunayeMukaman da za su iya samu
1.Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano) Ministan noma da raya karkara
2.Tsohon Gwamna Nyesom Wike Ministan harkokin cikin gida
3.Dr Kayode Fayemi Ministan harkokin waje
4.Farfersa Peter Okebukola (Tsohon sakataren NUC) Ministan ilimi
5.Mallam Nuhu Ribadu (tsohon shugaban EFCC) Ministan harkokin yan sanda
6.Sanata Aisha Binani Ministar wutar lantarki
7.Babatunde Ogala Atoni Janar na Tarayya
8.Wale Edun Ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa
9.Mofe Boyo Ministar man fetur
10.Ayo Abina Karamin ministan tsare-tsare na kasa
11.Femi Gbajabiamila Shugaban ma’aikatan shugaban kasa
12.Yewande Sadiku Ministar masana’antu
13.Yemi Oke, Farfesar Makamashi/Lantarki
14.Iyin Aboyeji, shugaban Flutterwave
15.Dayo Israel, Shugaban matasan APC na kasa
16.Misis Uju Ohanenye, tsohuwar yar takarar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Tsare-tsaren Tinubu ga wadanda ka iya samun mukaman majalisa, majiya ta bayyana

Bugu da kari, majiyar ta ambaci cewa mutanen da ka iya samun mukamai a majalisar na iya shiga cikin tawagar kula da tattalin arziki.

Har ila yau, ana iya ba wasun su mukaman shugabanci a hukumomin tattara kudaden shiga masu muhimmanci.

A cewar majiyar, shugaban kasar ya fi son zabar yan jam'iyyar APC a majalisarsa da wasu muhimman mukamai. Sai dai kuma, yana duba yiwuwar shigo da wasu gogaggu daga wajen jam'iyyar wadanda ka iya taimaka masa wajen cimma manufarsa na farfado da tattalin arzikin.

Tinubu na iya taso yan chanji a gaba

A wani labarin, mun ji cewa Asiwaju Bola Tinubu ya fara daukar tsauraran matakai tun bayan rantsar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Idan har ya yi nasarar cike tallafin mai, ana ganin mutane na gaba da Shugaban kasa Tinubu zai sako a gaba sune yan chanji masu hada-hadar kudi a kasauwar bayan fage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng