Ganawar Tinubu da Kwankwaso: Ganduje Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Tinubu Ya Bashi Mukami
- Tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba ya neman wani mukami a sabuwar gwamnatin Bola Tinubu
- Gwamna Ganduje ya fadi hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyi lokacin ganawa da manema labarai ranar Talata
- Ganduje ya kara da cewa idan har an bashi wani mukami a gwamnatin ba zai ki karba ba, tunda su suka kafa gwamnatin
Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce baya bukatar wani mukami a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da aka rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata 30 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai.
Ganduje ya yi bayani akan yiyuwar yin aiki tare da Tinubu duk da alakar da ke tsakaninsa da Kwankwaso, inda ya ce idan aka bashi wani matsayi ba zai ki karba ba, cewar Legit.ng.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Ba na neman wani mukami a wannan gwamnati, amma idan aka bani wani matsayi ba zan ki karba ba.”
Ganduje ya yi fatan nasara ga gwamnatin Tinubu
Ganduje ya yi fatan samun nasara ga gwamnatin Tinubu kamar yadda mutane suka zabe shi don suna tunanin zai kawo abubuwan ci gaba ga kasar kamar yadda ya yi a jihar Lagos, cewar rahotanni.
Menene ainihin abin da jawo wannan martani
Martanin gwamnan na zuwa ne bayan da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka gana da sabon shugaban kasa Bola Tinubu a kwanakin baya.
A wani sabon murya da aka nada, an jiyo Ganduje yana nuna damuwarsa akan ganawar da Bola Tinubu ya yi da Sanata Kwankwaso a birnin Paris, yayin da gwamna Ganduje ya yi fatali da muryar da aka nada da cewa an kirkire ta ne don kawo matsala a tsakaninsa da Tinubu.
Abba Gida Gida Ya Kori Dukkan Wadanda Ganduje Ya Nada Mukami
A wani labarin, Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin sallamar dukkan wadanda Ganduje ya ba su mukamai.
A wata sanarwa da aka sanyawa hannu, gwamnan ya ce dukkan shugabannin kananan hukumomi da kamfanoni su ajiye aikinsu.
Asali: Legit.ng