Ana Wata Ga Wata: Hadimin Atiku Ya Taya Tinubu Da Shettima Murna Bayan Rantsar Da Su
- Siyasar kasar ya dauki wani sabon salo yayin da Daniel Bwala, hadimin Atiku Abubakar, ya taya shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima murna
- A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne Tinubu da Shettima suka dauki rantsuwar kama aiki karkashin jagorancin shugaban alkalan Najeriya, Justis Olukayode Ariwoola,a Eagles Square
- Da yake daukar rantsuwa, Tinubu ya sha alwashin yin gaskiya da kuma bin kundin tsarin mulkin Najeriya
A wani yanayi da za a iya kira da sabon salo, Daniel Bwala, hadimin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya taya sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar kama aiki.
Yan mintoci kadan bayan rantsar da Tinubu da Shettima a matsayin shugabanni, Bwala ya garzaya shafinsa na Twitter don taya sabbin shugabannin na Najeriya murna.
Hadimin Atiku ya taya Tinubu da Shettima murna
Ya roki Allah ya ba sabbin shugabannin hikima da karfin gwiwar shugabantar kasar da kyau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rubuta a shafin nasa:
"Bari na taya Bola Ahmed Tinubu @officialABAT da Kashim Shetima @KashimSM murnar daukar rantsuwar kama aiki da mubaya'a a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasar Najeriya na 16 don kare kundin tsarin mulki da kuma jan ragamar kasar Najeriya. Ina rokon Allah madaukakin sarki ya baku hikima da karfin shugabantar wannan kasa mai albarka da gaskiya da amana. Ina taya ku murna ba tare da la'akari da siyasa ba."
Kalli bidiyon lokacin da Buhari ya bar Abuja zuwa Daura
A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa, Aisha sun bar Abuja, babban birnin tarayyar kasar jim kadan bayan mika mulki ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Buhari da matarsa sun samu rakiyar wasu manyan jami'an gwamnatinsa zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Tsohon shugaban kasar na Najeriya ya bar Eagle Square, Abuja bayan ya mika mulki shugaban kasar Najeriya na 16 sannan daga nan ya shiga jirgin saman sojoji mai lamta 001 zuwa Katsina a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa da ke Daura.
Asali: Legit.ng