Zargin Kisan Kai: Sabon Gwamnan Kano Ya Sha Alwashin Sake Waiwayar Shari’ar Doguwa
- Sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin sake waiwayen shari'ar Ado Doguwa
- Abba gida-gida ya ce za su bibiyi shari'ar zargin kisan kai da ake yi da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai har zuwa karshenta
- Ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan Kano a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce zai gurfanar da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassa Doguwa, wanda ake zargi da kisan kai, Premium Times ta rahoto.
Abba Gida-Gida ya sha wannan alwashin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Kano.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Doguwa
Ana zargin Doguwa da harbi da kashe mutane uku yayin wani rikicin zabe tsakanin magoya bayansa da mambobin jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP) a karamar hukumar Tudun Wada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika an kona ofishin jam'iyyar NNPP a yayin rikicin.
A farkon watan nan ne tsohon Atoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Musa Lawan, ya ce gwamnati ta soke tuhumar kisan kai da yan sanda ke yi wa Doguwa.
Ya ce gwamnatin ba za ta iya tuhumar dan majalisar da kisan kai ko kone-kone ba.
Mista Lawan ya bayyana hakan ne bayan rundunar yan sanda ta gabatar da rahoton bincikenta kan lamarin ga gwamnatin Jihar Kano domin ta yi nazari a kai da yiwuwar hukunta Doguwa da wasu 14.
Doguwa wanda ya kasance dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya zargi yan sanda da son kai, wanda ya yi sanadiyar sake nazari kan binciken hukumomin yan sandan.
Ana zargin Doguwa da kisan mutane uku yan jam'iyyar adawa ta NNPP yayin zaben ranar 25 ga watan Fabrair yayin da rigima ta kaure tsakanin yan NNPP da APC.
Abba Gida-Gida ya sha alwashin sake bude shari’ar Ado Doguwa
Sai dai sabuwar gwamnatin jihar karkashin jagorancin jam'iyyar NNPP ta ce za ta sake bude shari'ar har sai an kai karshen ta.
Abba Gida-Gida ya ce:
"A wannan kafar za mu binciki duk shari'a na rikicin siyasa da ya kai ka rasa rayuka da kayayyaki a fadin jihar a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Jaridar Daily Nigerian ta kuma nakalto shi yana ci gaba da cewa:
“Za a ci gaba da shari’ar Alhassan Ado Doguwa, kan zargi da ake yi masa na daukar nauyin raunatawa tare da kashe mutane sama da 15 a karamar hukumar Tudun Wada har zuwa karshensa."
Abba Gida-Gida ya yi nade-nadensa na farko a kujerar mulki
A wani labarin, mun ji cewa sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada mukaman farko a ofis.
A wata sanarwa da ta fito ta ofishin Sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan Kano ya sanar da mukarrabansa.
Asali: Legit.ng