“Cikin Kwanaki 60”: Faleke Ya Magantu Kan Bayyana Ministocin Tinubu
- Dan majalisar wakilai, James Faleke, ya bayyana lokacin da gwamnatin Bola Tinubu mai shigowa za ta bayyana ministocinsa
- Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana cewa za a sanar da mambobin majalisar Tinubu cikin kwanaki 60 bayan rantsar da shi
- Faleke ya bayyana hakan ne yayin hira da Channels TV a wajen bikin rantsar da shugaban kasar, a Eagle Square, Abuja
Abuja - Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. James Faleke, ya bayyana lokacin da sabon shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, sai bayyana ministocinsa.
Faleke ya bayyana cewa zababben shugaban kasar zai sanar da ministocinsa cikin kwanaki 60 bayan rantsar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Nigerian Tribune ta rahoto.
Dan majalisar tarayyar mai wakiltan mazabar Ikeja kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai kan kudi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV a Eagle Square, Abuja.
Faleke ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Shakka babu, cikin kwanaki 60, abun da doka ta ce kenan. Yana iya sanarwa a duk lokacin da ya so amma abun da na sani dole ya aikata hakan cikin kwanaki 60."
Manyan nade-nade 3 da ake sa ran Tinubu zai yi jim kadan bayan rantsar da shi da wadanda zai iya nadawa
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kamar yadda yake bisa al'ada, ana sa ran zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai sanar da nade-nadensa jim kadan bayan ya dauki rantsuwar kama aiki karkashin jagorancin shugaban alkalai, Justice Olukayode Ariwoola.
Wadannan manyan nade-nade na da muhimmanci don tabbatar da tafiyar gwamnati ba tare da tangarda ba yayin da ake jiran sauran nade-nade da ke bukatar yardan majalisar dokokin tarayya.
Gwamna Bagudu ya yi manyan nade-nade kafin mika mulki
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamna mai barin gado na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya yi sabbin nade-nade yan awanni kafin ya mika mulki.
Bagudu ya nada sabon shugaban ma'aikatan jihar Kebbi da wasu sakatarorin din-din-din guda hudu yayin da yake shirin mika mulki ga Nasiru Idris, zababben gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng