Tuna Baya: Dalilin da Yasa Buhari Ya Ki Yin Jawabin Rantsarwa a Shekarar 2019
- A shekarar 2019, Shugaba Buhari ya zo da sabon abu inda yaki gabatar da jawabi a ranar rantsarwa bayan zabanshi karo na biyu
- Jam’iyyun adawa da dama sun caccaki shugaban inda suka bayyana yadda ya dauki ‘yan Najeriya ba da muhimmanci ba
- Ko zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai bi tsarin da shugaba Buhari ya yi na daga jawabin har sai 12 ga watan Yuni?
FCT, Abuja – Ana yin jawabin rantsar da sabon shugaban kasa ko kuma zababben shugaban kasa a karo na biyu a bikin kaddamar da sabuwar gwamnati wadda shugaban kasa zai yi a yayin bikin.
Bikin yana da matukar muhimmanci wadda ke kawo karshen wata gwamnati da kuma shigowar sabuwar gwamnati don ganin kamun ludayinta.
Jawabin mafi yawanci yana dauke da manufofi da tsare-tsare na gwamnatin wanda zai kawo karshen matsalolin kasar da kuma kawo damarmaki wa ‘yan kasa.
Jawabin yana kara hada kan ‘yan kasa da kwarin gwiwa da kuma hada karfi da karfe don kawo karshen matsalolin da ke damun kasa, Legit.ng ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yaushe aka fara?
Yin jawabi a yayin kaddamar da sabuwar gwamnati ko karo na biyu ya zama kamar al’ada tun a baya lokacin jawabin Sir. Abubakar Tafawa-Balewa.
Tafawa-Balewa ya yi jawabin farko a kasar ranar 1 ga watan Oktoba 1960, yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da nashi a shekarar 2015 da sabon salo inda ya ke cewa “Ni na kowa ne, kuma ni ba na kowa ba ne”.
Har ila yau, bayan zabansa da aka yi a shekarar 2019, Buhari ya kafa tarihi inda yaki gabatar da jawabi a karon farko a kasar.
Me Buhari ya yi a ranar rantsarwar?
A lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2019, Buhari rantsuwa kawai ya yi da kuma duba fareti na jami’an tsaro daga bisani ya shige motarsa ya tafi.
Jam’iyyun adawa da dama sun koka kan yadda Buhari yaki gabatar da jawabi, inda suka ce hakan ya nuna rashin kulawa da ko oho ga ‘yan Najeriya.
Me yasa Buhari bai gabatar da jawabin ba?
Bayan cece-kuce da ake ta yi akan rashin gabatar da jawabin, wata majiya daga fadar shugaban kasan da Daily Trust ta tattaro ta ce jawabin kaddamarwar za a gabatar da ita ne a ranar Dimukradiya wato 12 ga watan Yuni.
Kafin rantsarwar, gwamnatin tarayya ta daga yin jawabin zuwa 12 ga watan Yuni.
Abin da ba a sani ba shi ne ko zababben shugaban kasa Bola Tinubu shi ma zai daga jawabin zuwa ranar 12 ga watan Yuni.
Rantsar Da Bola Tinubu: Rantsuwar Kama Aiki, Jawabi, Mika Mulki Da Buhari Zai Yi
A wani labarin, yayin da wa'adin Shugaba Muhammadu Buhari ya zo karshe, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai karbi ragamar mulki a hukumance a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Bikin rantsarwar za a yi shi ne a farfajiyar Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng