“Ka Shafe Kujerar Karamin Minista”: Malamin Addini Ya Shawarci Tinubu Gabannin Rantsar Da Shi

“Ka Shafe Kujerar Karamin Minista”: Malamin Addini Ya Shawarci Tinubu Gabannin Rantsar Da Shi

  • Shugabannin addinai sun fara martani ga bikin rantsar da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa wanda za a yi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, inda suka gabatar da bukatunsu
  • Imam Abdulrafiu Busari, mataimakin babban limamin garin Ayobo na so zababben shugaban kasar ya mayar da hankali ga ma'aikatar ilimi
  • Rabaran Ebenezer Egbebunmi na cocin Foursquare Gospel da keMegida Ayobo ya bukaci Tinubu da ya rage kudaden da ake kashewa a gwamnati sannan ya yi aiki da matasa

Shugabannin addinai a fadin kasar sun fara taya Bola Tinubu, zababben shugaban kasa murna gabannin rantsar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Wasu jerin shugabannin addinai da suka zanta da Legit.ng suna so Tinubu ya magance matsalar balaguro da mata ke yi, rashin aiki da kuma rage tsadar gwamnati da farfado da ma'aikatar ilimi.

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

Bola Tinubu
“Ka Shafe Kujerar Karamin Minista”: Malamin Addini Ya Shawarci Tinubu Gabannin Rantsar Da Shi Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Dalilin da yasa akwai bukatar Tinubu ya yi aiki da matasa a bangaren fasaha da noma

Rabaran Ebenezer Egbebunmi, wani babban fasto a cocin Foursquare Gospel, Megida Ayobo, Lagas, ya bukaci shugaban kasa mai jiran gado da ya rage tsadar gwamnati sannan ya mayar da hankali wajen tallafawa matasa don kawar da aikata laifuka a tsakanin jama'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Ina sa ran zababben shugaban kasa zai fuskanci gaskiya sannan ya tauna tsakuwa wajen rage tsadar gwamnati da kuma shafe mukaman kananan ministoci. Zan ba shugaban kasa mai jiran gado shawarar ya dunga bitar kokarin ministocinsa duk bayan shekaru biyu sannan ya sauya wadanda basu tabuka abun kirki ba da wasu.
"Ina mai umurtan Tinubu da ya yi aiki da matasa sannan ya tallafa masu a bangaren fasaha da noma, ya bari su fahimci tsare-tsaren gwamnati don su daina guduwa sauran kasashe a fadin duniya. Ya kuma yi aiki kan tsadar abubuwa."

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Jerin Manyan Matsaloli 5 da Ke Jiran Tinubu da Zarar Ya Karbi Buhari

Tinubu ya ba bangaren ilimi fifiko, Limamin Lagas

A nasa bangaren, Imam Abdulrafiu Busari, mataimakin limamin garin Ayobo da ke Lagas, ya bukaci shugaban ksar da ya kewaye kansa da masu bashi kyawawan shawarwari saboda gwamnati ba abu ne na mutum daya ba.

Malamin Musuluncin ya bukaci Tinubu da ya zamo mai sauraron koken mutane da kuma kula da ma'aikatan gwamnati.

Ya kuma ce:

"Gwamnati ba za ta iya raba mana kudi ba, gwamnati ba za ta iya siya mana kayan sawa ba amma akwai wasu abubuwa da ya kamata ma'aikatar ilimi da sauransu su kula da su.
"Wannan ya kasance ne saboda da zaran an sanar da kowa da ilimantar da kowa, zai zama kamar tallafi ne kan duk abun da mutum yake yi."

Legit.ng ta ji ta bakin wasu yan kasa game da wannan bukatu inda suka nuna goyon bayansu ga haka, suna masu cewa idan har Tinubu ya bi wannan shawarwari zai ga haske a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu Bai Musluntar da Matarsa Ba Balle Ya Musluntar da Najeriya, Inji Kashim Shettima

Mallam Hassan Muhammad ya ce:

"Muna kyautatawa gwamnatin Bola Tinubu zato, saboda mun ga abun da ya yi a matsayin gwamnan Lagas don a nan aka haife ni kuma na taso. Amma duk da haka wannan magana ce ake yi ta kasa ba jiha ba dole akwai aiki ja a gabansa. Amma kamar yadda malaman nan suka fadi, idan ya kafa majalisa ta kwararrun mutane da za su ba shi shawara da fada masa gaskiya komai dacinta lallai za a samu nasara. Allah ya yi masa jagora, Allah kuma ya albarkaci kasarmu Najeriya.

A nasa bangaren Isyaku ya ce:

"Lallai ya kamata a Tinubu ya janyo matasa a jiki domin samun nasara a wannan sabuwar gwamnati mai kamawa. Matasa sune jigon ci gaban kowace al'umma, a basu ilimi mai inganci, a basu tallafi don dogaro da kai. Da zaran an yi haka za ka nemi rashin tsaro da ya yi wa kasar katutu ka rasa saboda dama rashin aiki ne yake kawo su."

Kara karanta wannan

Uhuru Kenyatta Ya Ba Tinubu Muhimman Shawarwari Gabannin Rantsar Da Shi

Yan Najeriya sun zabi shugaba nagari da Tinubu, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna kwarin gwiwa cewa Najeriya za ta inganta a karkashin gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Buhari ya ce yan Najeriya sun yi zabi mai kyau domin Tinubu ne ya fi cancanta a cikin dukkanin yan takarar da suka nemi kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng