"Ku Dauki Kaddara Kan Hukuncin Da Kotu Za Ta Yi", Shugaba Buhari Ga 'Yan Adawa

"Ku Dauki Kaddara Kan Hukuncin Da Kotu Za Ta Yi", Shugaba Buhari Ga 'Yan Adawa

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga jam'iyyun adawa da su kai zuciya nesa su rungumi hukuncin da kotu za ta yi kan ƙararrakin zaɓe
  • Shugaba Buhari ya buƙace da su zo a haɗa hannu da su domin samar da Najeriya wacce za ta kasance abin alfahari
  • Shugaban ƙasar mai barin gado ya kuma yaba musu kan yadda suka kai ƙorafe-ƙorafen su a gaban kotu domin neman haƙƙinsu

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayun 2023, ya buƙaci jam'iyyun adawa da su rungumi hukuncin da kotu za ta yi kan ƙararrakin zaɓe, cewar rahoton The Punch.

Jaridar Leadership tace, shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na bankwana, da ya yi wa ƴan Najeriya a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Yana Dab Da Sauka Mulki, Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Abu Da Ya Faru Da Shi Wanda Bai Taba Tunani Ba

Shugaba Buhari ya yi kira ga jam'iyyun adawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto : Channels Television
Asali: Twitter
"Duk ta yadda hukuncin ƙararrakin ya kasance, ina roƙon duk jam'iyyun da abin ya shafa da su karɓi hukuncin da kotu ta yi, sannan su haɗa hannu wajen gina Najeriya da za a yi alfahari da ita." A cewarsa.

Shugaba Buhari ya yi irin wannan kiran a baya lokacin da ya aike da saƙon Easter, a ranar 7 ga watan Afirilu, inda ya roƙi ƴan Najeriyan da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni, bai yi musu daɗi ba, da su haƙura su bar kotuna su yi aikinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya yabawa jam'iyyun adawa

Shugaba Buhari ya yaba da juriya da jajircewar da dukkanin ƴan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyunsu suka nuna, ta hanyar kai ƙorafe-ƙorafen su kan sakamakon zaɓen zuwa gaban kotu.

A kalamansa:

"A lokacin yaƙin neman zaɓe, mun yi musayar ra'ayi kan yadda za a ciyar da Najeriya gaba, amma ba mu taɓa samun bambantar ra'ayi ba ko wata tantama cewa yakamata Najeriya ta fi haka ci gaba."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

"A matsayina na shugaban ƙasar ku, ina kira a gare mu da mu tattaro dukkanin ƙarfin mu, ƙarfin haɗin kan mu, da imanin da mu ke da shi domin ciyar da Najeriya gaba."

Ban Taba Tunanin Zan Zama Shugaban Kasa Ba - Buhari

Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ɓai taɓa tunanin mulkar ƙasar nan ba.

Shugaba Buhari wanda zai bar madafun iko a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya mulki ƙasar nan dai a mulkin soja da na farar hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng