Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasa Buhari Zai Gabatar Da Jawabin Bankwana Ga 'Yan Najeriya

Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasa Buhari Zai Gabatar Da Jawabin Bankwana Ga 'Yan Najeriya

  • Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, zai yi jawabin ƙarshe ga ƴan Najeriya ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 7 na safe
  • Hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad, shine ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter, ranar Asabar 27 ga watan Mayu
  • Sanarwar na zuwa ne ana sauran ƴan sa'o'i kaɗan shugaba Buhari ya miƙa ragama mulkin ƙasar nan a hannun Bola Tinubu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, zai yi jawabin bankwana ga ƴan Najeriya, a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayun 2023.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad, na Twitter @BashirAhmaad, ya fitar wacce Legit Hausa ta ci karo da ita a ranar Asabar, 27 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Karrama Tinubu, Shettima Da Babbar Lambar Yabo Ta Kasa, Kwana 4 Kafin Ya Bar Ofis

Shugaba Buhari zai yi jawabin bankwana ga 'yan Najeriya
Shugaba Buhari zai gabatar da jawabin bankwana a matsayin shugaban kasa Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabin bankwanan ne ga ƴan Najeriya da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe.

Sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabin bankwana na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa, babban kwamandan askarawan Najeriya, a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 7 na safe."

Kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin sanarwar, an buƙaci kafafen watsa labarai da su haska jawabin bankwanan na shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

"Gidajen talbijin, gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labarai su kama gidan talbijin Nigerian Television Authority (NTA) da gidan rediyon Radio Nigeria domin haska jawabin." A cewar sanarwar

Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban ƙasa, ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, bayan ya shekara takwas cif yana mulkin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Ku Koma Ofis," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Lokacin da Zasu Sauka Daga Mulki

Sarkin Musulmi Ya Aike Da Muhimmiyar Shawara Ga Bola Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, mai alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya aike da muhimmiyar shawara ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Mai alfarma sarkin Musulmin ya shawarci Bola Tinubu da ya mayar da hankali wajen kawo ci gaban ƙasa, a maimakon ya fara tunanin yadda zai sake ɗarewa kan shugabancin ƙasar nan a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng