"Dole Ka Taimaki Najeriya Don Dawo Da Martabarta a Duniya": Kenyatta Ga Tinubu
- An bukaci zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da ya shirya ma gagarumin aikin da ke gabansa a matsayin shugaban kasa
- Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ne ya bayar da wannan umurni a wajen taron rantsarwa a Abuja
- Ya bayyana Tinubu a matsayin uban kowa kuma jagoran hada kan da ji gaban Najeriya
Abuja - Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya bayyana cewa akwai babban aiki ja a gaban zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yayin da ake shirin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.
Kenyatta ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu, a wajen taron rantsarwa wanda aka yi a Abuja don karrama zababben shugaban kasar.
Tsohon shugaban kasar Kenyan ya ce aikin Tinubu ya girmi tunanin mutane da dama, kasancewar yanzu shine "uban kowa" kuma"alamar hadin kai" ga Najeriya da nahiyar Afrika.
Kamar yadda Channels TV ta rahoto, ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da zaran ka kama aiki a matsayin shugaban kasa, za ka yi hikima idan ka tsallake siyasar dabarar cin zabe sannan ka kama aiki a matsayin mai yi wa Najeriya hangen nesa.
"Wannan zai bukaci sauya tunanin adawar da mu yan siyasa ke runguma a lokacin tsarin zaben.
"A matsayin shugaban kasa, ya zama dole ka koyi abubuwa cikin sauri don jagorantar wadanda suke sonka da wadanda basa sonka da zuciya daya da kuma jajircewa saboda yanzu, kai uban kowa ne."
Ya kuma bukaci Tinubu da ya zama cikin shiri domin shine zai gyara rabuwar kai na kabilanci da addini wanda ya afku a shekarun baya, yana mai cewa ya zama dole ya nemi abokan hamayya domin cika wannan hadin kai.
Kenyatta ya bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta gyara kura-kuranta sannan ta hau kan matsayinta a duniya, jaridar The Sun ta rahoto.
Ganawa da ma'aikatan fadar shugaban kasa da wasu muhimman abubuwa 3 da Tinubu zai yi bayan rantsar da shi
A wani labarin, mun ji cewa akwai wasu muhimman abubuwa da ake sanya ran zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai aiwatar da zaran an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.
Daga cikin wadannan abubuwa, ana sanya ran zai nada hadimansa, shugaban ma'aikatansa da sauransu.
Asali: Legit.ng