Gwamna Ganduje Ya Nada Sabon Kwamishina Yana Dab Da Barin Mulki
- Gwamna mai barin gado na jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa sabon kwamishina a jihar yana dab da barin ofis
- Gwamna Ganduje ya naɗa Abdullahi Abba Sumaila a matsayin sabon kwamishinan hukumar zaɓe ta jihar
- Naɗin kwamishinan na zuwa ne yayin da ya rage saura ƴan sa'o'i kaɗan gwamna Ganduje ya bar madafun iko
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi sabon naɗin kwamishina yana dab da yin bankwana da kujerar mulkin jihar Kano.
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa, gwamna Ganduje a ranar Juma'a ya rantsar da sabon kwamishinan hukumar zaɓe ta jihar.
Rantsar da sabon kwamishinan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan gwamnan ya umurci dukkanin masu riƙe da mukaman siyasa a jihar, da su ajiye muƙamansu zuwa ranar Juma’a.
Abdullahi Abba Sumaila, ya zama sabon kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), bayan ya yi rantsuwar kama aiki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rantsuwar kama aikin sabon kwamishinan ta gudana ne a zaman majalisar zartaswar jihar na ƙarshe a daren ranar Juma'a, 26 ga watan Mayun 2023.
Ganduje ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje lokacin da yake jawabi bayan rantsar da sabon kwamishinan, ya ce an ba kwamishinan rantsuwar kama aiki ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta tantance shi.
Ganduje ya ce bayan tantancewar da majalisar ta yi masa, ta kuma amince da aka naɗa shi muƙamin kwamishina.
Gwamnan ya buƙace shi da ya yi aiki yadda ya dace saboda girman muhimmancin da hukumar ta ke da shi a jihar Kano.
A kalamansa:
"Muna fatan cewa zaka gudanar da aikin ka yadda ya dace saboda muhimmancin da kujerar da aka baka ta ke da ita, musamman wajen gudanar da zabukan ƙananan hukumomi a jihar Kano."
Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Ya Bayyana Kadarorinsa Gabanin Rantsar Da Shi
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Gida-Gida ya bayyana kadarorin da ya mallaka a duniya.
Gwamnan mai jiran gado ya bayyana kadarorinsa ne a gaban hukumar kula da. Ɗa'ar ma'aikata, yayin da ake shirin rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Kano.
Asali: Legit.ng