Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Ya Bayyana Kadarorinsa Gabanin Rantsar Da Shi

Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Ya Bayyana Kadarorinsa Gabanin Rantsar Da Shi

  • Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana kadarorinsa a gaban hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa (CCB), reshen jihar Kano
  • Ya bayyana kadarorin nasa ne yau Juma'a, kwanaki uku gabanin a rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Kano
  • Abban a yayin da yake bayyana kadarorin, ya kuma tabbatar da cewa duka mutanen da zai bai wa muƙaman gwamanti suma za su zo don bayyana nasu kadarorin

Kano - Gabanin rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida ya bayyana kadarorinsa.

Abba ya bayyana kadarorin ne yau Juma'a a ofishin hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa (CCB) reshen jihar Kano, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Abba ya samu tarba daga daraktar hukumar ɗa'ar ma'aikata ta jihar Kano, Hajia Hadiza Larai Ibrahim.

Zababben gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya bayyana kadarorinsa
Zababben gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya bayyana kadarorinsa. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Alama ce ta gaskiya da riƙon amana

Abba ya ce wannan bayyana kadarorin da ya yi na nuni da gaskiya da riƙon amana da zai zama ginshikin gwamnati mai kamawa a jihar Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma ƙara da cewa bayyana kadarorin wani haƙƙi ne da kundin tsarin mulkin ƙasa ya rataya masa na bayyana kadarorin kafin shiga ofis.

A kalamansa:

“Alhamdulillah. A yau na bayyana kadarorina a cikin wani kundi da na gabatarwa hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa reshen jihar Kano (Code of Conduct Bureau).
“A yayin da mu ke jiran gabatowar ranar 29 ga watan Mayu don karɓar rantsuwa, wannan bayyana kadarorin zai kasance wata hanya ta nuna gaskiya da riƙon amana wadda zai zama ginshiƙin gwamnati mai zuwa ta Jihar Kano a karkashin jagorancina. - AKY”

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Muƙarraban Abba ma za su bayyana kadarorinsu

Abban ya kuma bayyana ta hannun sakataren yaɗa labaransa Sunusi Bature Dawakin Tofa, cewa ko sisin kobo ba zai yi ciwo ba daga kuɗaɗen asusun jihar Kano a ƙarƙashin mulkinsa.

Ya kuma ba da tabbacin cewa, dukkan jami’ai waɗanda suka haɗa da masu rike da muƙaman siyasa da za su yi aiki a gwamnatinsa, za a ba su izinin bin tsarin bayyana kadarori kamar yadda doka ta tanada.

Buhari ya bayyana kadarorinsa, ya umarci muƙarrabansa su bayyana

A wani labarin mai kama da wannan da muka wallafa a baya, kun ji cewa shugaban ƙasa mai barin gado Muhammadu Buhari ya bayyana kadarorinsa ga hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata (CCB) ta ƙasa da ke Abuja.

Ya bayyana kadarorin nasa ne ranar Juma'a a ofishin hukumar da ke Abuja. Buhari ya kuma umarci duk muƙarabansa da suka yi aiki tare da su zo su bayyana nasu kadarorin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng