Daga Wurin Mika Mulki Zan Wuce Kaduna Kafin Tafiya Daura, Shugaba Buhari

Daga Wurin Mika Mulki Zan Wuce Kaduna Kafin Tafiya Daura, Shugaba Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce daga filin da ya miƙa mulki, zai wuce kai tsaye zuwa jihar Kaduna
  • Buhari ya ce zai sanya hannu a kan wasu takardu a karshen makon nan amma ya ƙosa ranar Litinin ta zo
  • Ya kuma bayyana yadda kasashen duniya suka aminta da babban zaben 2023 wanda gwamnatinsa ta shirya

Abuja - Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ranar Jumu'a ya ce yana miƙa mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023, nan take zai hau jirgi zuwa jihar Kaduna.

Buhari ya ce daga filin Eagle Square da ke Abuja, inda zai miƙa wa zababben shugaban kasa ragamar mulki, ba zai jira ya kwana ba zai wuce Kaduna, daga bisani ya tafi Daura, jihar Katsina.

Shugaba Buhari.
Daga Wurin Mika Mulki Zan Wuce Kaduna Kafin Tafiya Daura, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ya ce a kowace rana yana ƙirga kwanakin da suka rage domin ya ƙosa ranar Litinin ta yi ya sauka daga kujera lamba ɗaya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Kadarorinsa, Ya Ce Babu Wanda Zai Tsira a Mukarrabansa Bai Bayyana Nashi Ba

Shugaban ya ce zai yi amfani da ranakun ƙarshen mako domin rattaɓa hannu a kan wasu takardu da zasu ba shi dama daga filin miƙa mulki, ya ɗare jirgi ya bar Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wace jiha Buhari zai fara sauka bayan barin Abuja?

Buhari ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da littafin da aka rubuta da sunansa, wanda ya ƙunshi nasarorin gwamnatin Buhari tun daga 2015-2023 a Aso Villa.

A kalamansa, shugaba Buhari ya ce:

"Ina tunanin a tsawon lokacin da na ɗiba ina aiki, na shafe shekaru 20 a rundunar soji, ban yi mamaki ba, domin idan ka yi niyyar ba mutane mamaki, kai a karan kanka zaka ji daɗi."
"A zahirin gaskiya ban taɓa tsammanin haka ba, musamman a yau da nake buƙatar sa hannu a wasu takardu saboda na san daga wurin rantsarwa ranar Litinin, zan tashi a jirgi zuwa Kaduna, daga nan na tafi ɗayan ɓangaren Najeriya."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jirgin Saman Najeriya Ya Shirya Kamo Hanya Zuwa Birnin Tarayya Abuja, Bidiyo

Shugaban ƙasan ya kara da bayanin cewa ƙasashe da dama daga Turai da Amurka sun kira shi suna taya shi murnar nasarar zaben 2023 da aka kammala.

FG ta ba da hutun rantsarwa

A wani labarin na daban Gwamnatin Buhari ta ayyana hutun kwana 1 saboda bikin rantsar da zababben shugaban ƙasa Bola Tinubu.

FG ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023 a matsayin ranar hutu ga kowane ɗan kasa.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce hakan zai bai wa kowa damar murnar rantsar da sabon shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262