Wasu Daga Cikinku Sun Mun Zagon Kasa a Lokacin Zabe, Gwamna Sule Ga Hadimansa

Wasu Daga Cikinku Sun Mun Zagon Kasa a Lokacin Zabe, Gwamna Sule Ga Hadimansa

  • Gwamna Sule ya faɗa wa kwamishinoni da sauran mambobin majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa cewa ya san abinda ya faru lokacin zaɓe
  • A cewarsa, ya samu labarin wasu daga kinsu sun yi iya bakin kokarinsu domin kar ya samu nasarar tazarce a kan kujerar gwamna
  • Sule ya kuma sanar da rushe majalisar baki ɗaya, ya umarci kwamishinoni da hadimai su sauka daga muƙamansu

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwan gwamnatinsa sun masa zagon ƙasa a kokarin neman tazarce.

Sule ya tona wannan sirri ne a wurin taron bankwana da baki ɗaya mambobin majalisar wanda ya gudana a gidan gwamnati da ke Lafiya ranar Alhamis.

Gwamna Sule.
Wasu Daga Cikinku Sun Mun Zagon Kasa a Lokacin Zabe, Gwamna Sule Ga Hadimansa Hoto: Gov Abdullahi Sule
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bayan faɗin waɗanda suka yaƙi kudirin tazarcensa, Gwamna Sule ya sanar da rushe majalisar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamna Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Umarni Nan Take

A cewarsa, yana da damar korar waɗanda suka yake shi jim kaɗan bayan kammala zaben amma da gangan ya zuba musu ido suka ci gaba da aiki karkashinsa har zuwa karshen zangon farko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Sule ya ce:

"Karo na karshe da muka zauna taro makamancin wannan shi ne a lokacin ana gab da zaɓe, na gayyace ku muka nemi goyon bayanku, mun buƙaci ku taimaka ku yi duk me yuwuwa domin mu samu nasara."

Gwamna ya faɗi waɗanda suka masa zagon ƙasa

Abdullahi Sule ya faɗa wa mambobin majalisar da ta ƙunshi kwamishinoni da hadimai cewa ya samu labarin waɗanda suka goyi bayansa da masu yaƙarsa.

"Na gani da ido na kuma na samu labarin da yawanku kun yi aiki ba dare ba rana don tabbatar da mun samu nasara a babban zaɓe."
"Haka nan na gani kuma na samu labarin wasu daga cikinsu sun hana idonsu bacci, sun yi aiki kamar ba gobe don kawai suka mun sha kashi a zaɓe."

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

"Ina miƙa godiya ta gare ku musamman waɗanda suka taimaka mana muka sake cin zabe, suka yi kunnen uwar shegu da duk wasu maganganu. Tsoron Allah da cika ranstuwarku ne suka kaimu ga nasara."

Bana tunanin sauya sheka daga PDP - Gwamna Ortom

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ortom Na Jihar Benue Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC.

Gwamnan Benuwai na ɗaya daga cikin mambobin tawagar G-5, tare da wasu gwamnoni 4 daga kudancin Najeriya, waɗanda suka yaƙi takarar Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262