Gwamna Ortom Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

Gwamna Ortom Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce yana nan daram a PDP kuma baya shirin sauya sheƙa a nan kusa
  • Ortom ya tabbatar da cewa ya goyi bayan jam'iyyar adawa a lokacin zaben shugaban ƙasa amma yana nan a cikin PDP
  • Haka nan ya bayyana cewa zai goyi bayan sabuwar gwamnati mai kamawa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya musanta yuwuwar cewa wata rana zai tattara kayansa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan.

Ortom ya sha alwashin goyon bayan shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, domin bunƙasa tsarin Demokuradiyyar Najeriya.

Gwamna Ortom.
Gwamna Ortom Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Hoto: Samuel Ortom
Asali: UGC

Gwamnan ya ƙara da cewa yana cikin waɗanda suka yi fafutukar mulki ya koma kudu bayan shugaba Buhari ya ƙarisa wa'adinsa a 2023.

Kara karanta wannan

"Najeriya Zata Ƙara Bunkasa," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Tinubu Wasu Kalamai Masu Kyau

Mista Ortom ya yi wannan jawabin ne ranar Laraba 24 ga watan Mayu, 2023 a wata hira da kafar watsa labaran Arise TV cikin shirin Morning show.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Benuwai na ɗaya daga cikin mambobin tawagar G-5, tare da wasu gwamnoni 4 daga kudancin Najeriya, waɗanda suka yaƙi takarar Atiku Abubakar.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa gwamnonin G-5 sun ɓalle daga inuwar PDP kana suka nemi shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus domin yin adalci da daidaito.

A rahoton This Day, Ortom ya ce:

"Wannan baya gabana, ina nan daram a PDP, na yi aiki tuƙuru domin mulki ya koma kudu, wanda Obi da Tinubu suna ciki, sauya sheƙa ba ya gaba na a yanzu."
"Idan aka rantsar da Tinubu, zan mara masa baya kuma na masa fatan samun nasara . Ina nan a matsayin jagoran PDP a jihar Benuwai amma zan ci gaba da kokarin tabbatar da adalci da daidaito a Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Najeriya Zata Ƙara Bunkasa a Mulkin Bola Tinubu, Shugaba Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya ce yana da yaƙincin Najeriya zata ci gaba da bunƙasa karkashin shugabancin Boƙa Ahmed Tinubu.

Buhari ya yi wannan furuci ne a wurin bikin karrama Tinubu da lambar girmamawa mafi daraja GCFR a taƙaice da kuma karrama Kashim Shettima a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262