"Ko Ka Tsaya A Daura Ko Ka Tafi Nijar Za Mu Neme Ka": Tinubu Ga Buhari

"Ko Ka Tsaya A Daura Ko Ka Tafi Nijar Za Mu Neme Ka": Tinubu Ga Buhari

  • Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa za a dunga neman gudunmawarsa a duk inda yake bayan barin mulki
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga furucin da shugaban kasar ya yi cewa watakila Nijar zai koma da zama bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu
  • Da yake jawabi bayan karrama shi da lambar yabo ta kasa, Tinubu ya fada ma Buhari cewa ya sa ran jin sallama a kofarsa, imma a Daura, Nijar koma a duk inda yake

Abuja - Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya fada ma shugaban kasa Muhammadu cewa za su neme shi a duk inda zai gudu ya je bayan barin kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Da yake martani ga furucin da shugaban kasar ya yi a ranar Talata, 23 ga watan Mayu cewa Nijar za ta cece shi idan wani ya biyo shi bayan ya bar mulki a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana cewa a duk inda shugaban kasar zai koma bayan mulkinsa, ya sa ran amsa kira.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
"Ko Ka Tsaya A Daura Ko Ka Tafi Nijar Za Mu Neme Ka": Tinubu Ga Buhari Hoto: Bayo Omoboriowo
Asali: Twitter

Abun da Tinubu ya fada ma Buhari bayan karbar lambar yabo ta GCFR

Zababben shugaban kasar ya yi furucin ne yayin da yake jawabi bayan karrama shi da lambar yabo ta GCFR tare da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda aka karrama da GCON.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng ta bibiyi taron karramawar a tashar TVC a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Tinubu ya kuma bayyana cewa yana sane da tarin kalubalen da ke gabansa da zaran ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Ya kuma godema shugaban kasar kan karrama shi da mataimakinsa da lambar yabo ta kasa.

Ya ce:

"Ka yi iya yinka, ya mai girma shugaban kasa. Yanzu, babban aiki zai hau kaina. Na san ma'anar lambar yabon da aka bani a yau da kuma girman aikin da ke jirana. Ko ka tafi Daura, Nijar, ko ko'ina, ka sa ran jin sallama a bakin kofarka."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Komawar Shugaba Buhari Nijar Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Ba zan ba yan Najeriya kunya ba, Bola Tinubu

A wani labarin, shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai ci amanar 'yardar da shugaba Muhammadu Buhari da miliyoyin 'yan Najeriya suka masa ba.

Ya kuma jaddada cewa ya fahimci girman lambar gurmamawan da aka karrama shi da ita kuma ya san muhimmancin aikin da ke gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng