Majalisa ta 10: 'Yan Majalisar Jam'iyyun Adawa 63 Sun Goyi Bayan Tajuddeen Abbas Da Kalu
- Zaɓaɓɓun 'yan majalisu na adawa 63 sun goyi bayan 'yan takarar da jam'iyya mai mulki APC, ta tsaida a neman shugabancin majalisar
- Kakakin gamayyar 'yan majalisun na adawa, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana haka a wani taro a Abuja
- Jam'iyyar APC ta tsaida Abbas Tajuddeen da kuma Benjamin Kalu a matsayin shugaban majalisa da mataimakinsa
Abuja - Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai 63 na jam’iyyun adawa sun amince da ’yan takarar jam’iyya mai mulki, wato Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa.
Kakakin gamayyar jam’iyyun adawar, Ikenga Ugochinyere, wanda ya jagoranci zaɓaɓɓun mambobi 62 na 'yan adawa, ya sanar da amincewarsu a Abuja ranar Laraba, in ji rahoton Punch.
An nemi sauran masu takarar su janyewa Abbas
Ugochinyere, zaɓaɓɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Ideato ta Arewa da ta Kudu, ya yi kira ga sauran masu neman kujerar kakakin majalisar da su janye daga takarar, domin kuwa ba za su samu kuri’u ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ikenga ya yi kira ga masu neman kujerar da su marawa tikitin Abbas da Kalu baya don samun shugabancin da zai kawo ci gaban da ya fi na majalisun baya.
Ya kuma ce ya kamata yanzu duk a ajiye siyasar jam'iyyanci, a zo a haɗa kai don ciyar da ƙasar gaba.
Ikenga ya ce Abbas da Kalu sun cancanta
Sannan ya ce zaɓin Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu zaɓi ne da aka yi sa bisa cancanta da gogewa.
Sannan ya ce duka mambobin adawa 62 da ke tare da shi sun aminta da hakan domin manufofinsu ɗaya ne, kuma ra'ayinsu ne yake faɗa a madadinsu.
Kakakin ƙungiyar ya kuma ƙara da cewa, Tajuddeen Abbas ya haɗa duk abubuwan da ake buƙata domin zama shugaban majalisa.
A rahoton jaridar Leadership, Ikenga ya ce Tajuddeen ne ya fi kowane dan majalisa kawo kuduri a gaban majalisa ta tara da ke karewa.
'Yan majalisu na ruwan daloli domin neman shugabanci
A wani labarin namu na baya, kun karanta cewa wasu 'yan majalisu na ta barin daloli ga abokan aikinsu domin su zabesu a zaben shugabancin majalisar da ke karatowa.
An ce wasu daga cikin sanatocin da ke neman shugabancin majalisar dattawa ne ke ta rabon kudin domin samun goyon baya.
Asali: Legit.ng