Ahmad Lawan Ya Musanta Takarar Kujerar Shugabancin Majalisar Dattawa Ta 10
- Shugaban majalisar dattawa sanata Ahmad Lawan ya nesanta kansa da sake neman shugabancin majalisar
- Rahotanni sun yi yawo kan cewa sanatan ya shiga tseren neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10
- Ahmad Lawan ya ce ƙarya ce zallarta kawai ake bibiyarsa da ita, domin baya da niyyar sake maimaita shugabancin majalisar dattawa
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan, ya musanta cewa yana da aniyar yin tazarce a kujerar shugabancin majalisar dattawa.
Ahmad Lawan, cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo suna cewa yana neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, ƙarya ce tsagwaronta, rahoton The Nation ya tabbatar.
Dole ta sanya fito ya bayyana gaskiya
Sanatan ya ce bai yi niyyar yin magana akan rahotannin ba, amma sai ya lura da cewa idan bai ƙaryata su ba, za a iya ɗauka kamar da gaske ne, cewar rahoton TVC News.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Na karanta wasu rahotanni masu cewa na shiga tseren neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10. Ban yi niyyar yin magana akai ba, amma idan ana barin ƙarairayi na yawo, ba tare da musanta su ba, za su iya sanyawa a ga kamar akwai gaskiya a cikinsu.
"Maganar gaskiya itace ɓan taba gayawa wani ko yin taro da wani ba, kan cewanl ina neman shugabancin majalisar dattawa ta 10. Saboda haka ina kiran mutane da su yi watsi da waɗannan rahotannin."
"Zance na gaskiya shine har yanzu ina cikin shugabannin jami'yyarmu ta APC, inda mu ke ƙoƙarin nemo mafita kan matsalolin da suka taso kan shugabancin majalisa ta 10. Zan cigaba da mayar da hankali na akan hakan."
Sanata Sani Musa Ya Musanta Goyon Bayan Ahmad Lawan
A wani rahoton na daban kuma, sanatan jam'iyyar APC mai wakiltar Niger ta Gabas a majalisar dattawa, ya nesanta kansa da takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10, ta Ahmad Lawan.
Sanata Sani Musa, ya bayyana cewa sharri ake masa na cewa yana daga cikin masu ƙulla-ƙullar ganin sanata Ahmad Lawan, ya yi tazarce a shugabancin majalisar dattawa.
Sanatan ya ce ko kaɗan babu hannunsa a ciki, inda ya bayyana cewa yana kan matsayar da suka cimmawa da takwarorinsa kan shugabancin majalisar.
Asali: Legit.ng