Majalisa Ta 10: Abbas, Kalu Da ’Yan Majalisu 30 Sun Dira a Abuja Don Ganawa Da Adamu

Majalisa Ta 10: Abbas, Kalu Da ’Yan Majalisu 30 Sun Dira a Abuja Don Ganawa Da Adamu

  • Abbas Tajudden da Benjamin Kalu sun dira a sakatariyar jam’iyyar APC don taro da kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar
  • Abbas da Kalu dai samu isa wurin taron tare da wasu ‘yan majalisu har 30 domin tattauna wasu muhimman abubuwa
  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar shi ne zai jagoranci wannan taro da ya kasance na farko

Abuja - Honarabul Abbas Tajudeen da Honarabul Benjamin Kalu da jam’iyyar APC ta zaba a matsayin wadanda za su gaji kujerar majalisar wakilai suna sakatariyar jam’iyyar a Abuja da wasu ‘yan majalisa 30 don ganawa da kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar.

Taron wanda zai gudana a sakatariyar a yau Talata 23 ga watan Mayu, ana saran zai gudana tare da shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Abbas Tajudden da Benjamin Kalu
Honarabul Abbas Tajudden da Honarabul Benjamin Kalu. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Wannan shi ne karon farko da Abbas da kuma Kalu za su tattauna tun bayan da jam’iyyar ta zabe su a matsayin masu gadan shugabancin kujerar majalisar wakilai a ranar 8 ga watan Mayu, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Lissafi Zai Koma Sabo a APC, Ahmad Lawan Zai Iya Shiga Takarar Majalisar Dattawa

Rahotanni sun tabbatar da cewa a kujerar majalisar wakilai an zabi Abbas Tajudden a matsayin shugaba yayin da Benjamin Kalu zai kasance mataimakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Felix Morga ya sanar da matakin jam'iyyar

An sanar da umarnin jam’iyyar ne ta bakin sakataren yada labaran jam’iyyar, Felix Morka bayan shafe fiye da sa’o’i uku ana tattaunawa da kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar.

Wannan hukunci na jam’iyyar ya jawo cece-kuce musamman daga sauran ‘yan majalisar da suke da sha’awar tsayawa takara, inda suka koka cewa jam’iyyar ba ta tuntubi kowa ba yayin yanke wannan hukunci.

Har yanzu ba a san musabbabin yin taron ba

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a san takamaimai abubuwan da za su tattauna a yayin taron ba.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar cewa taron ba zai wuce karin haske ga shugaban jam’iyyar APC din ba game da irin nasarorin da suka samu yayin neman goyon baya daga sauran ‘yan majalisun.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar PDP v Tinubu da Shettima

Dalilin da ya sa Arewa maso Yamma ta Samu Shugabancin Majalisar Wakilai

A wani labarin, Ana sa saran Abbas Tajudden da Benjamin Kalu za su gaji kujerar majalisar wakilai ta tarayya.

Honarabul Abbas Tajudden ya bayyana cewa Arewa maso Yamma ba a banza ake ba su matsayi a majalisun ba saboda muhimmancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.