Kotun Zabe Ta Amince da Bukatar Atiku Na Gabatar da Shaidu 100 a Mako 3
- Kotun zaɓe a Najeriya ta amince da buƙatar Atiku ta gabatar da shaidu akalla 100 cikin makonni uku
- Mai shari'a Haruna Tsammani ya bayyana cewa Kotun ta haɗe kararrakin guda uku wuri ɗaya domin hanzarta yanke hukunci
- A ƙarar da ya shigar, Atiku ya buƙaci Kotu ta umarci janye shaidar cin zaben da INEC ta baiwa zababben shugaban kasa
Abuja - Kotun sauraron ƙarar zabe mai zama a Abuja ta baiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar PDP da zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, mako uku kamar yadda ya buƙata.
Ƙotun ta amince da bukatar Atiku wanda ya nemi mako uku domin gabatar da shaidu akalla 100 da zasu yi gamsasshen bayani kan cewa Bola Tinubu na APC ba shi ne sahihin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa ba.
Da yake karanta rahoton kararrakin, shugaban kwamitin alkalan Kotun, mai shari'a Haruna Tsammani, ya ce jumullan shaidu 166 ake sa ran zasu ba da shaida kan batun.
A rahoton Vanguard, Alkalin ya ware wa hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kwanaki biyu ta kare kanta, kana ya baiwa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da APC kwanaki 5 kowane ya kare kansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotu ta haɗe ƙararrakin wuri ɗaya
Bugu da ƙari, Kotun ta yanke cure baki ɗaya kararraki uku da suka ƙunshi ƙarar Peter Obi, APM da kuma Atiku Abubakar wuri ɗaya domin hanzarta yanke hukunci.
Alkalin da ya karanta rahoton ya yi bayanin cewa haɗe kararrakin wuri ɗaya zai taimaka wajen tabbatar da an yi gaskiya kan ƙorafe-korafen, kamar yadda Punch ta rahoto.
A cewarsa, bayan wannan lokaci, kowane ɓangaren zai gabatar da jawabinsa na ƙarshe, daga bisani kuma Kotu ta sanya ranar yanke hukunci.
Atiku ya nemi a kwace shaidar cin zaɓe daga hannun Tinubu
A ƙarar da Atiku ya shigar mai lamba CA/PEPC/05/2023 ya roki Kotu ta ba da umarnin janye shaidar cin zaben da INEC ta baiwa zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Ya jaddada cewa ayyana Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa, "bai halatta ba saboda saɓa wa tanadin kundin dokokin zabe 2022."
A wani labarin na daban kuma Kotu Ya Yanke Hukunci Baiwa Peter Obi Wa'adin da Zai Gabatar da Shaidu Kan Kalulabalantar nasarar Bola Tinubu.
Mai shari'a Tsammani ya bayyana jadawalin yadda zaman Kotun zai gudana har zuwa ranar yanke hukunci kan sahihancin zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng